Tsaffin Daliban KTC sun Ziyarar Shugaban Hukumar Jin dadin Alhazai ta jihar Katsina
- Katsina City News
- 28 Dec, 2023
- 413
KATSINA TEACHERS COLLEGE OLD BOYS.
A ranar laraba 27/12/2023 kungiyar tsoffin daliban Kwalejin horar da Malamai ta Katsina watau National Alumni Association of Katsina Teachers College karkashin jagorancin Alh Kabir Lawal Ruma ta ziyarci sabon Babban Daraktan hukumar jin dadin Alhazai ta Jihar Katsina Alh Yunusa Abdullahi Dankama domin isar da takardar taya murna a gareshi a madadin dukkan tsoffin daliban Makarantar.
Makarantar kwalejin horar da Malamai ta Katsina makaranta ce mai dumbin tarihi da aka kafata a shekarar 1922 watau shekaru dari da daya kenan da suka wuce.
Makarantar ta yaye dalibai da dama a ciki da wajen Jihar Katsina wanda a halin yanzu tana da dalibai sama da dubu goma sha hudu.
Tawagar ta samu rakiyar elder a cikin tsoffin daliban Alh Usman Tunau wanda ya kammala a shekarar 1974, Alh Yusuf Kankara shugaban reshen daliban yan shekarar 1979, Shu'aibu Abdullahi Jani, Abdullahi Lawal K/Bai da Sakataren kungiyar tsoffin daliban ta kasa Abubakar Umar Nasarawa.
Da yake bayani kafin mika ma Babban Daraktan Hukumar Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama takar dar Taya murna da fatan Alheri Shugaban tawagar Alhaji Kabir lawal Ruma ya Shaida Babban Daraktan cewa sunzo ne gurinshi domin taya shi murna tare da Yi mashi fatan Alheri da kuma Neman goyon bayan shi akan kudirin kungiyar na hada kawunan sauran mambobin ta domin cigaban makarantar.
Ya kuma roki Babban Daraktan da ya isar ma kungiya da godiya da jinjina ga maigirma gwamnan jihar katsina Mallam Dikko Umar Radda akan baiwa tsofin daliban makaran tar kusan su Goma mukamai a gwamnatin shi.
Alhaji Kabir lawal Ruma Wanda yayi dogon bayani akan halin da makarantar take tare da Bayyana wasu Nasarori da kungiyar ta samu wajen tallafama makarantar har ma da daliban makarantar.
A Nashi Jawabin Babban Daraktan Hukumar Jin dadin Alhazai ta jihar Katsina Alhaji Yunusa Abdullahi Dankama yayi godiya da wannan karramawa da sukayi mashi tare da tabbatar masu da cewa a shirye yake da Koda yaushe domin tallafama kungiyar tare da basu goyon baya domin kafa Babban kungiyar ta tsoffin daliban makarantar.
Yayi masu fatan Alheri tare da jinjina masu akan kokari su na hadin kan tsoffin daliban makarantar tare da Yi masu fatan Alheri akan kudirin Nan nasu.PRO PWBKT.