SARAUTAR MAGAYAKIN KATSINA.
- Katsina City News
- 26 Dec, 2023
- 776
Sarautar Magayaki tana daya daga cikin Sarautun Tsaro ko Kuma Sarautun Yaki a Katsina. Idan dai ba a manta ba Sarakunan Habe sune suka kawo ko Kuma suka shinfida tsarin Sarautu na Gargajiya a Katsina, Wanda ya faro daga Sarki Muhammadu Korau(1348-1398) zuwa Sarakunan da suka biyo bayan shi. Daga cikin wannan Tsarin Sarautunne aka samu Sarautun Tsaro, da suka hada da 1. Kaura, Wanda shine babban kwamandan babbar rubdunar Yaki, baya Kaura akwai sauran kwamandojin Yaki irin su 2. Magayaki da 3. Uban dawaki da sauransu. Misali a Yakin Katsina da Gobir a shekarar 1795, Wanda yayi sanadiyyar Mutuwar Sarkin Gobir Yakuba, Kauran Katsina Kuren Gumari shine ya jagorancin Yakin( YB Usman).
Sarautar Magayaki tana daya daga cikin manyan Sarautu a Kasar Hausa shiyyasa ba kowa ake ba itaba, Sai Jarumin gaske, Wanda baya shafuwa a fagen Yaki.
Tun daga mulkin Dallazawa har zuwa yanzu anyi Sarautar Magayaki da dama a Katsina, Wanda gidaje da dama suka riki wannan Sarauta ta Magayaki. Daga cikin wadanda sukayi Sarautar Magayaki akwai:--
1. Magayaki Mamman Gajeran Bade. Kamar yadda Dr. Yusuf Bala Usman yayi bayani Acikin littafinshi Mai suna the Transformation of Katsina, Mamman Gajeran Bade Yana daga ckin Badawan da suka zo Katsina daga Kasar Bade, a farko farkon karni na (19 ). Yayi Sarautar Shantali, Sarkin Bai, Ajiya, Wanda daga baya lokacin Sarkin Katsina Ibrahim aka nadashi Magayakin Katsina a shekarar 1871. Gajeran Bade ya taimaka wajen yake yaken da Katsina da Maradi a farkon karni na (19). Yana daya daga cikin mayakan Katsina da suka fatataki Danbaskore daga shiyyar Ingawa ta Katsina.
Wasu daga cikin Zuruar Gajeran Bade sun hada da. 1. Senator Hadi Sirika, former Minister for Aviation. 2. Ahmed idris Yamel. 3. Marusan Katsina. 4. Alh. Kabir Yau Yamel( Sarkin Aikin Kasar Hausa. 5. Alh. Abba Yusuf ( Chairman Makera Motels da sauransu).
2. Magayaki Muhammadu Nasamu( Kofar Bai). Baya ga Gajeran Bade Sai Kuma Magayaki Nasamu. Muhammadu Nasamu kamar yadda Bala Usman ya nuna Babarbarene, yazo Katsina daga Kukawan Borno, a lokacin Mulkin Dallazawa. Yayi Sarautar Dankafin Katsina, Ajiya, Sarkin Bai, Wanda daga baya aka nadashi Magayakin Katsina. Muhammadu Nasamu shine kashin bayan ginuwar Unguwar Kofar Bai. Daga cikin zuruarshi akwai:-- 1. Mariganyi Alhaji Bello Kofar Bai( Magayaki). 2. Alhaji Aminu Bello Kofar Bai( Magayakin Katsina na yanzu). 3. Justice Aminu Tukur Kofar Bai. 4. Mariganyi Alhaji Kasimu Kofar Bai. Da sauransu.
3. Magayakin Katsina Kwalale.
Muhammad Kwalale mutumin Kasar Auto ne dake cikin Kasar Hadejia. Yazo Katsina a karshe karshen mulkin Dallazawa. Ya taimaka wajen yake yaken da Katsina tayi da sauran abokan gabarta na wannan lokacin, musamman a lokacin Sarkin Katsina Abubakar (1887-1905) da Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (1906-1944).
Muhammadu Kwalale yayi Sarautar Magayaki daga shekarar 1887 zuwa 1907.
Muhammadu Kwalale ya rike Sarutu da dama kamin yayi Magayaki misali, Sarautar daya Fara rikewa itace ta Tarno a Kasar Jani lokacin Sarkin Katsina Ibrahim Dan Bello, Sai Kuma Sarkin Katsina Abubakar yayi masa Sarautar Ajiya.
Daga cikin Zuruar Magayaki Kwalale akwai. 1. Mariganyi Shanaki Ammani( Shamakin Katsina lokacin Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo). 2. Mariganyi Ummaru.Kadarko. 3. Alhaji Said Barda( tsohon Gwamna Jihar Katsina da sauransu.
A zamanin Sarkin Katsina Muhammadu Kabir Usman, har zuwa yanzu, wadanda sukayi Sarautar Magayaki sun hada da.
1. Magayakin Katsina late M. K. O Abiola (13-4-1991).
2. Magayakin Katsina late Bello Kofar Bai.
3. Magayakin Katsina Aminu Bello Kofar Bai. Shine Magayaki na yanzu, shi Kuma ya fito daga zuruar Magayaki Muhammadu Nasamu Kofar Bai.
Sourse.
1 YB Usman. The Transformation of Katsina ( 1400-1883) Ahmadu Bello University press LTD
2. Magayakin Katsina Kwalale. (1834-1929). Jamlad international resources Nigeria LTD. Katsina. 2015.
3. Tarihin Unguwannin Birnin Katsina. Katsina State History and Culture Bereaw. 2011.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.