AL,ADUN GIDAN SARKI, AKAN DOWOWAR MAI MARTABA SARKIN KATSINA DAGA WATA KASA.
- Katsina City News
- 26 Dec, 2023
- 748
AL,ADUN GIDAN SARKI, AKAN DOWOWAR MAI MARTABA SARKIN KATSINA DAGA WATA KASA.
Ga Al,ada a duk lokacin da Sarkin Katsina yayi tafiya daga Kasar shi zuwa wata Kasa, ko Kai ziyara ko don duba lafiyar shi da sauran. Akan shirya Al,adu da dama.
Shi dai Mai Martaba Sarkin Katsina Dr. Abdulmumini Kabir Usman yayi tafiysne zuwa Kasar Ingila domin duba lafiyar shi. Kuma ana sa ran zai dawo gida Katsina a ranar Litinin 31- 10-22. Allah ya Kara ma Sarki Lafiya.
Shi dai Sarki Abdulmumini shine Sarki na 50, tun daga Sarakunan Durbawa/Habe har zuwa Fulani. Kuma shine Sarki na 12 daga Fulani Sarakunan Katsina. Kuma shine Sarki na 4 daga zuruar Sarakunan Sullubawan Gidan Sarki Muhammadu Dikko.
An haifi Sarkin Katsina Dr. Abdulmumini Kabir Usman a ranar 9 ga watan Junairu na shekarar 1952. Yayi karatun shi na Primary daga shekarar 1959-1964. Daga nan wuce Makarantar Secondary ta Government Secondary School Katsina( wadda ake cema Dikko College yanzu) daga shekarar 1965-1969. Daga nan ya halarci Jamiar Ahmadu Bello dake Zaria daga shekarar 1972-1974. Ya samu Degree dinshi a Jamiar Usman Danfodio dake Sokoto daga shekarar 1978-1981. Yayi aikin bautar kasa (NYSC) da kamfanin Sokoto Rima River basin development daga shekarar 1981-1982. Daga nan Sai ya fara aiki na Dan lokaci da Kamfanin Sokoto Rima Riva basin development Company a shekarar 1982. A cikin watan December 1982 ne aka nada shi Sarautar Magajin Garin Katsina.
Acikin Shekarar 2008 ne aka nada Mai Martaba Sarkin Katsina a matsayin Sarkin Katsina, bayan rasuwar mahaifinsa Sarkin Katsina Dr. Muhammad Kabir Usman. Ya samu lambobin yabo da dama.
Ga kadan daga CI gaban da Sarki Abdulmumini ya kawo a Masarautar Katsina.
1. Ya Gina Islamiyya a Tabkin Lambu Kofar soro Mai suna DUKA ISLAMIYYA.
2. Ya kafa kungiyoyin Sintiri don samar da Tsaro a Unguwannin Cikin Birnin Katsina.
3. Yayi kokari na ganin cewa gwamnati ta bada sabon Matsugunni domin a maida Kasuwar Yarkutungu acan saboda cinkoson da take kawowa cikin Gari
4. Ya Kara karfafa wasan Kungiyar wasan Polo ta Katsina da dai sauransu.
GA AL'ADA IDAN SARKI YAYI TAFIYA MAI TSAWO DAWO GIDA, ANA GUDANAR DA A'ADU KAMAR HAKA.
1. TAKKAI. TAKKAI wata Al" adace wadda matasa Zasu hadu ana kidi ana rawa ana kada itace.
2. Dubar
Wani lokaci akan shiya wasan Durba domin nuna murna ga dawowar Mai Martaba Sarki Gida. Wannan Hawan Durba ya shafi Tawagar Sarki ta ranar Hawan Sallah kadai.
3. KADA TAMBARI.
So da yawa idan Sarki yayi tafiya ya dawo Sarkin Tambura zaizo da mutanen shi domin kadama Sarki Tambari. Ga AL'ADA shi dai Tambari ana kada shi a yanayi kamar haka.
1. Kada Tambari idan an nada sabon Sarki ko Kuma daya daga Hakimman Karaga.
2. Hawa da kada Tambari a yayin wani buki Wanda Sarki ya jagoranta
3. Yin sati guda ana kada Tambari a Kofar gidan Sarki a lokacin Bukin Sallah.
4. Akan kada Tambari idan Sarki yayi tafiya daga Kasar shi zuwa wata Kasa, idan ya dawo gida.
Al'ADA ta karshe ta dawo Sarki daga wata Kasa itace ta Yan Ishiriniyya. Yan Ishiriniyya kanzo gidan Sarki su rera Ishiriniyya.Marigayi Sarkin Katsina Dr. Muhammadu Kabir Usman mutum ne Mai shaawar Ishiriniyya, wannan dalilin mane yasa ya nada shugaban Yan Ishiriniyya watau MADAHA.