WASIYYAR UBA CIKIN HIKIMA
- Katsina City News
- 24 Dec, 2023
- 628
Akwai wani mutum da dansa karami. Kullum cikin dare yakan rika yi masa wa'azi a sha'anin zama da mutane. Tun yaro bai balaga ba sai Allah ya yi wa uban rasuwa. A ranar karshe kafin ya mutu sai ya ce da dansa, "Watakila Ciwon nan nawa ba na tashi ba ne. Saboda haka akwai wasiyyoyi da nake So in gaya ma amma zatin ciwo ba zai bari ba. Don haka in na rasu ka je wajen tsohon doki, kiyashi, kumurci da kare za su gaya maka abinda zan gaya ma'. Yana gamawa sai ya rasu. Bayan an gama zaman makoki sai yaro ya niyyata ya tafî wurin tsohon doki ya gaya masa sakon mahaifinsa.
Tsohon doki ya ce, "Lallai mahaifinka ya yi maka wasiyya mai kyau. Ka gan ni a nan ko turkena ba a share ba. Har yanzu ban karya kumallo ba. Ruwan sha sai na yi haniniya a kai a kai ake tunawa da ni. Wai kawai domin na tsufa. Lokacin kuruciyata ba abinda ba a yi min. In an hau ni ina nagarta har fitowa ake yi ana kallona, ana guda. Amma yanzu ina! Don haka komai za ka yi, ka yi lokacin kuruciyarka. Wannan shi ne dalilin wasiyar mahaifinka. Sauka lafiya."
Daga nan yaro bai zarce ko'ina ba sai wajen kiyashi. Ya gaya masa sakon ubansa. Kiyashi ya ce, "Lallai akwai wasiyya kuwa. Biyo ni ka ga abinda yake nufi." Suna cikin tafiya sai suka yi kacibis da mushen kyankyaso. Kiyashi ya ce, "Ka ga wannan mushe ba shakka ya raba ni fiye da dari a gırma. Saboda. haka ba zan iya jansa in kai ramina ba, bayan kuma ina so saboda abincina ne." Yaro ya ce, "I, gaskiya ne." Kiyashi ya ce, "Tsaya ka gani. Sai ya je ya kirawo kiyasai yan uwansa rututu. Nan da nan suka gewaye mushen kyankyaso suka ja giriri har cikin raminsu. Yaro ya ce, "To, me ke nan?" Kiyashi ya ce, "Komai za ka yi kada ka yi kai kadai sai da jama a, jama' ar, kuma taka. Wannan shi ne wasiyyar mahaifinka." Yaro ya yi godiya ya tafi wurin kare, ya gaya masa abinda ke tafe da shi.
Kare ya ce, Zo mu je. Kare ya wuce gaba yaro yana bi shi har suka zo wata makarantar allo mai almajirai da yawa an hura wuta ana ta karatu. Daga tsayawansu sai aka fara jifan kare ana, "Kolo", Kolo. Da kyar suka tsere. Ba su tsaya a ko ina ba sai gidan wani mafarauci. Daga ganin kare sai aka ba shi abinci, aka goge masa jiki, aka daura masa fata a wuya.
Kare ya ce da yaro, "To ka gani, lokacin da muka je makaranta ba a yi wata wata ba sai aka kore mu; amma da muka zo gidan mafarauci ga irin alherin da aka yi mana. Saboda haka komai za ka yi a duniya ka yi tare da masoyinka a inda ake son ka".
Yaro ya yi sallama da kare ya tafi neman inda Kumurci ya ke. Da kyar ya same shi a cikin wani kogon kuka. Ya gaya masa abinda ya kawo shi. Kumurci ya ce, Babu shakka babanka mutum ne mai tsinkaya. Yanzu ka gan ni nan a boye. Ba na fita da rana. Kuma ko daddare sai an yi barci don in ba haka ba da an gan ni sai a bi ni da duka a kashe ni. Ka san dalili?
Yaro ya ce, "A a". Kumurci ya ce, Harshena da bakina, su suka jawo min wannan bala'i. Don haka ka kiyayi harshenka da, bakinka. Abinda babanka yake son gaya ma ke nan."
Yaro ya yi godiya ya yi sallama ya tafi.
Wace wasiyya ce ta fi ratsa ka?
Daga littafin Hikayoyin Kaifafa Zukata na Marigayi Malam Aminu Kano..