An Kai Hari A Garin Rinji Ta Batsari ...Mai Garkuwa Da Mutane Yazo Garin da Rana Tsaka Da Bulala don Bada Kashi ga wani Dan garin da ya raina masa Wayo
- Katsina City News
- 23 Dec, 2023
- 542
AN KAI HARI GARIN RINJI TA BATSARI
....shugaban barayin da Rana an zauna dashi
........yazo da Bulala da niyyar bugun wasu
......ya Sanya masu tarar sabon Babur
Daga Misbahu Ahmada Batsari
@ Katsina Times
Ɓarayin daji masu satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa sun kai hari ƙauyen Garin Rinji dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina, ranar lahadi 10/12/2023.
Maharan sun sace mutane bakwai (mata), amma bayan kwana ɗaya biyu suka kuɓuta, sauran biyar kuma na hannun su.
Ana cikin tattaunawa da ɓarayin dajin domin samun bakin zaren yadda za su sako sauran matan da suka tsare, sai suka ce dole sai an biya kuɗin hadda waɗan da suka kuɓuta(mata biyu), in ba haka ba za su sake kawo samame su kwashi mutane. Sunce a biya su kuɗin fansa naira miliyan ɗaya da rabi ga mata ukku, sauran biyu kuma a basu dubu ɗari biyar saboda an bayyana masu marayu ne.
Ana cikin wannan ja-in-ja, sai ɓarawon da ya jagoranci kai harin wanda ake kira Bako-bako ya shigo garin da rana tsaka, a ranar talata 19/12/2023, ya tara mutane ya bayyana masu cewa shi ya kama ƴaƴan su kuma ba zai sake su ba sai sun biya kuɗin fansa, sannan ya nemi wanda suke waya da shi akan maganar biyan kuɗin amma a lokacin baya nan, sai ya fiddo wata zungureriyar bulala yace yaso ya iske shi ya bashi kashi saboda yace ya raina masa wayau lokacin da suke waya kan yadda za su biya kuɗin fansa.
Sannan ya sanya ma mutanen garin tara, cewa su sayo masa sabon mashin(babur) saboda wai yaran garin sun yi masa ihu. wanda suka ƙiyasta kuɗin sa zai kai naira dubu ɗari bakwai, daga bisani suka kasa kuɗin naira dubu shida shida kowanne magidanci. Majiyar mu ta bayyana cewa da yaji labarin sun haɗa naira dubu ɗari shida sai yace idan kuɗin basu kai miliyan ɗaya ba, ba zai karɓa ba.
Dama dai wannn yankin na Garin Rinji dake arewacin Batsari wanda bai fi nisan kilomita 10 ba daga Batsari yayi fama da hare haren ƴan bindiga inda har ta kai ga sun miƙa ma bori kai ya hau domin ko wane lokaci ɓarayin na shigowa garin suyi abunda suka ga dama.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762