"A Yiwa Shugaba Tunibu Uzuri a Jinjirin Mulkinsa mai Watanni 7" Guru Maharaji Ya Roƙi 'Yan Nijeriya
- Katsina City News
- 21 Dec, 2023
- 470
Zaharaddeen Ishaq Abubakar
A yayin Bukin Cikarsa Shekaru 76 da Zuwa Duniya, Shugaban Addinin "One Love Family" da aka fi sani da "Guru Maharaji" Yayi kira ga 'Yan Najeriya da su yiwa Allah su dunga yiwa Shugabanni Uzuri, Cikakkiyar dama gami da Addu'a.
Guru Mazaunin Jihar Oyo a Unguwar Maharaji dake Birnin Badin ya kuma yi kira ga Shugaban Nigeriya Malam Bola Ahamed Tunibu da ya kyautata Kyakkyawar Alaka ga Manoma a fadin Nijeriya don rage tashe-tashen hankali.
Guru ya bukaci da a samar da wani bukin Manoma a hukumance da buga Mujalla ta hadin kai, don tabbatar da Adalci, a duk shekara.
Malamin Addinin mai shekaru 76 da haihuwa ya ja hankalin Gwamnati ba akan Manoma ba kawai hadda Tattalin Arziki, Ilimi Kiwon Lafiya da Tsaro.
"Jaririn Mulkin na Shugaba Tunibu bai Fara Tatata ba Balle ya balaga har ya isa daukar Zunubi" inji Guru.
A zantawar sa da Manema labarai a gidan sa na Addinin "One Love Family" dake Ibaden Nijeriya yayi fatan Alheri da Addu'a ga Nigeriya.