Yi wa mata auren wuri ya zo karshe a jihar Katsina, Dr. Halima Umar Kofar Sauri.
- Katsina City News
- 16 Dec, 2023
- 529
Daga Mohammad A. Isah
Sakatariyar hukumar Ilimi a matakin farko na kananan hukumomin jihar Katsina, Dr Hajiya Halima Umar Kofar Sauri ce ta bayyana haka a lokacin da take gabatar da jawabi a wani taron bada hutun Makaranta na zangon karatu na farko, a Makaranatar Firamare ta "Jabiru Abdullahi Memorial Primary School Garama", a ranar juma'ar nan.
Sakatariyar ta bayyana cewar, yanzu kam, sakamakon hanyoyin ci gabantar da Ilimi ta hanyar zamanantar da shi da gwamnati Malam Dr. Dikko Umaru Radda ta 6ullo da su fadin jihar, to auren wuri da ake yi wa mata a jihar ya zo karshe baki daya.
"Ya wa yara mata auren wuri ya zo karshe." In ji ta.
"Yaranmu za su ci gaba da yin karatu tun daga Firamare har Sakandare da taimakon gwamnatin jihar Katsina." Ta yi albishir
Maganar tata dai na zuwa ne biyo bayan musayar yawu da ya soma bayyana tsakanin hukumomi da wasu ba'alin Malamai da masu rike da Masarautun gargajiya dangane da wani shiri da Bankin duniya ya zo da shi a Nijeriya mai suna "AGILE" wanda zai ba wa yara Ilimi na musamman wanda kusan kashi 70% zai karkata ne ga mata, shirin da wasu Malamai da shugabannin gargajiya ke ganin akwai Lauje a cikinsa, musamman duba da yadda shirin ya fi ba wa mata muhimmanci, inda tuni suka soma sukar shi.