An sako ɗaliban Jami'ar Dutsin Ma da 'yan fashin daji suka sace
- Katsina City News
- 15 Dec, 2023
- 598
Rahotanni daga jihar Katsina, na cewa an sako ɗaliban Jami'ar Tarayya ta Dutsin Ma, bayan shafe sama da wata biyu a hannun 'yan fashin daji.
Shugaban makarantar Farfesa Arma Ya'u Hamisu Bichi, ya shaida wa BBC cewa ya samu labarin sakin sakin ɗaliban daga ɗaya daga cikin mahaifan ɗaliban da misalin ƙarfe huɗu na yamma.
Ya ƙara da cewa an saki duka ɗaliban huɗu da suka rage a hannun 'yan bindigar.
A ranar Laraba 4 ga watan Oktoba ne, wasu 'yan bindiga suka auka gidan kwanan ɗaliban - dukkansu mata - da ke zaune a wajen jami'ar cikin unguwar Maryama Ajiri da tsakar dare.
Sai dai daga baya 'yan bindigar sun saki guda ɗaya daga cikinsu.
Hukumomi dai sun ce suna ci gaba da tuntuɓa da tattaunawa don ganin an sako ɗaliban ba tare da wani lahani ba.
Lamarin ya faru ne ƙasa da mako biyu bayan sace wasu ɗalibai 'yan mata a Jami'ar Tarayya ta Gusau cikin jihar Zamfara mai maƙwabtaka.
Duka jihohin biyu suna fama da rikicin 'yan fashin daji waɗanda ke kai hari kan garuruwa da ƙauyuka tare da sace mutane don yin garkuwa da su da zimmar neman kuɗin fansa.
Shugaban Jami'ar ya shaida wa BBC cewa a iya sanin saninsa ba a biya diyya ba kafin a saki ɗaliban, sai dai ya gode wa mai bai wa shugaban ƙasa shawar kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, da kwamishin 'yan sandan jihar Katsina da daraktan hukumar tsaro ta DSS da ke jihar da karin wasu mutane, bisa ƙoƙarin da ya ce ya yi har aka kai ga sakin ɗaliban.