TAKAITACCEN TARIHIN GARIN WAGINI DA SARAUTAR GADO DA MASUN KATSINA.
- Katsina City News
- 15 Dec, 2023
- 1057
Garin WAGINI Yana cikin garuruwan Karamar hukumar Batsari ta yanzu. Shi wannan Gari an kafa shi tun wajen shekarar 1889, lokacin mulkin Dallazawa. Wanda yayi Jagorancin kafa Garin shine Dan- Ani, wannan shine dalilin da yasa ake ma Garin WAGINI Kirari da " WAGINI GARIN DAN- ANI, GARIN MAI DUBU. IDAN BA DUBUN HATSI BA DUBUN MUTUM, GARIN GIWA IDAN BA GIWAR DAWA BA GIWAR DAJI.
Shi wannan mutum Dan-ani asalinsa daga Kasar Nijae yake, ya baro can inda yake da zama tare da iyalinsa a sanadiyyar wani Yaki daya faru Kasar har ya shafi inda suke zama. A lokacin yakinne aka tarwartsa inda suke zama. Saboda wannan dalilin suka watse kowa ya Kama gabansa. Shi Kuma Dan- Ani tare da matarsa da wasu daga cikin danginsu, sukayi Shawarar suyi Kaura su sake wuri. Sai sukayi Kaura suka fado cikin Kasar Nigeria ta yanzu. Sun fara zama a wani wuri da ake cema Yasore Nan arewacin Kasar Batsari. Daga nan Sai suka lura wurin bai Dace dasu ba, don haka Sai suka bar wurin, basu tsaya koina ba Sai wurin da Garin WAGINI yake yanzu. Anan suka Fara kafa matsugunni. Dan- Ani da jamaasa manoma na gasken gaske. Basu da sanaar data wuce noma.
Shi Kuma sunan WAGINI ya Sami sunansane daga wata Korama wadda kenan Yammacin Garin. Wannan Korama itace WAGINI, daga bayane sunan Koramar ya rikide ya koma sunan Garin WAGINI kasancewar Koramar tana cikin Garin WAGINI.
Bayan da Turawan Mulkin Mallaka suka nada Sarkin Katsina Muhammadu Dikko sarautar Katsina Acikin shekarar 1907, Sai Sarki Dikko ya rinka rangadi Yana kewaya Kasarsa, Acikin irin wannan rangadinne wata rana Allah ya kaishi Wagini. Sarki ya iske wurin Kasar Noma ce Mai yalwa da amfani. Wannan abu da Sarki ya gani ya bashi shaaawa kwarai da gaske. Saboda haka Sai Sarki Dikko ya nada Danani Sarkin Noma. Daga nan Jamaa da dama suka ci gaba da zama Garin Wagini.
Dangane da abunda ya shafi Mulki Danani shine dagacin Farko na Wagini, daga shi Sai dansa Alu ya Gajeshi. Bayan rasuwar Alu Sai Sani ya Gajeshi.
Acikin shekarar 1992 ne aka daukaka matsayin Sarautar Wagini daga Sarautar Dagaci zuwa Hakimi da Kuma bata Sarautar Gado da masun Katsina. Hakimi na farko Wanda aka nada shine Alhaji Shehu Muazu Ruma, daya daga cikin yayan Sarkin Ruma Muazu. A halin yanzu Alhaji Dikko Muazu Ruma shine Gado da masun Katsina Kuma Hakimin Wagini.
Garin Wagini halin yanzu Yana da Magaddai kamar haka. 1. Magaji Wagini. 2. Magaji Manawa. 3. Magaji Madogara. 4. Magaji Abadau. 5. Magaji Kasai. 6. Ciroman Karare. 7. Magaji Nahuta. 8. Magaji Kagara. 9. Magaji Madaddabai.
Alhaji Musa Gambo Kofar soro.