TAKAITACCEN TARIHIN MUHAMMADU DURUGU
- Katsina City News
- 27 Aug, 2023
- 845
Wanda akafi sani da BABBAN GWANI
Daga shafin kasar zazzau jiya da yau.
Shi dai Muhammadu Durugu wanda aka fi sani da BABBAN GWANI wani mutum ne da ya yi rayuwar sa a garin zariya cikin birnin zazzau
.
Shi dai shararren magini ne wanda ubangiji ya bashi baiwa tin yana dan karami, ubangiji ya bashi baiwa yana iya daukan laka ya juyata zuwa abubuwa kala kala, saboda haka nema abokanan sa suka sa masa suna da GWANI saboda irin wannan fasaha da baiwa da Allah ya masa.
.
GIRMANSA: A na nan a har ubangiji ya sa ya girma ya zamto shahararren magini a birnin zaria. Muhammadu Durugu yayi rayuwar sa a karni na sha tara ne, lokacin da ya yi rayuwar sa har izuwa yau baa samu magini kamar sa ba a kasar hausa. Kuma baya gini sai dare yayi domin yana aiki ne da leburorin da suka kai ma mutane dari, ya kan umurce su da suyi ta kwaba kasa suna gyarata tsawon yini shikuma bazai tashi suwa ba sai dare ya yi. Yayin da dare yayi idan ya zo ya hau ya fara gini kafin wayewar gari wurin da al'umma suka barshi fili
.
Za su tashi suga gini a wajen ya tashi, kuma shi yake zane da kansa, shi ya ke fitar da wuri, shi yake trarin ginin da kan sa.
.
WURAREN DA YA GINA: Babban gwani Durugu ya yi gine gine na fadojin sarakuna da masallatai da dama a kasar hausa daga cikin su akwai fadan zazzau, fadan sarkin birnin gwari, yaje kasar bauci ya yi a garin karfen madaki, haka kuma ya yi gini a fadan kano. Masallatai kuwa akwai babban masallacin garin bauci na yanzu da kuma masallacin jumaar fadan me martaba sarkin zazzau.
.
Tarihi ya nuna cewa Durugu lokacin da yake wannan gine-gine akwai lokacin da yake gina masallacin zazzau, sarkin zazzau na wannan lokacin ya zo da kansa ya ga kamar be saka masallacin ya kalli alkibla ba, sarki ya zo ya masa magana yana cikin aiki ya ce" wannan masallacin da ake ginawa be kalli al'kibla dai - dai ba". Ya zo acikin tarihi babban gwani ya sakko ya dafa kafadan sarki ya nuna masa gabas, da ya kallah gabas a wannan lokacin sai ga KA'ABA kai tsaye.Maana kenan ya nuna masa aikin sa na kan dai dai. Wannan bai wace da Allah ya bashi wanda tasa sarki ya kalli al'kibla daga nan inda yake tsaye. Hakan yasa sarki ya tsorata ya sallama ma DURUGU.
.
Muhammadu Durugu shi kadai ya ke yin ginin sa, tarihi ya tabbatar lokacin da leburorinsa guda dari kowanne yakan jeho masa tobalin kasa har akan kai wani lokaci yakan ce musu "TO HAYYA MANA, KU YI SAURI MANA"
.
Mutane dari suna jeho masa kuma yana karba na kowanne baya faduwa kuma yana ce musu suyi sauri. Da wannan ne jaama sukega kamar aljanu suna sa masa hannu ya yin aikin sa. To amma babu wani abu na tarihi ko wani abu na zahiri da zaa iya tabbatar da hakan, kawai dai mutane sunyi tinanin hakan, amma dai shi Allah ya masa wannan baiwa.
.
Kuma har yanzu akwai ragowan gine ginan sa da har yanzu ake amfani da su, daga cikin su akwai masallacin jumaa da ke fadan sarkin zazzau.
.
Hakama zuri'ar sa, har yanzu akwai su a cikin birnin zazzau, daga cikin su akwai WAZIRIN MAGINA acikin birnin Zazzau kuma har yanzu suna yin wannan sanaar ta gini kuma da kasa suke yin ta duk da dai akwai wata hira da su da akayi sun bayyana yanzu jamaa sun karkata i zuwa gine ginen zamani, amma duk da haka har yanzu idan aka gaiyace su ginin kasa suna zuwa su yi, kuma idan suka yi ana samun inganci saboda baiwa da suka gada tindaga zamanin kakan nin su.
.
RASUWAR SA: Akwai abubuwa dama cikin rasuwar sa, amma tarihi ya bayyana ce wa yrasu a 1830, kuma rasuwa ce ba ta Allah ba domin kashe shi a kayi. Kuma ana tinanin kisan da da alaqa da wasu sarakuna wanda yamusu gine-gine suna gudun kar ya je ya sake yima wasu irin ginin ko kuma wanda ya fi nasu kyau.
.
Yanzu haka a cikin birnin zariya inda ya zauna sunan unguwan BABBAN GWANI kuma ragowan tsatson sa suna nan a gidan da ya zauna.
.
Muna fata Allah ya jikan magabatan mu
.
MANAZARCI : Dr Yakubu Magaji Azare ( malami a sashen koyar da harsuna a nigeria. A jami'ar Bayero da ke kano.
.
NOTE: WANNAN PHOTON BA NA DURUGU BANE, PHOTON WASU DAGA ZURU'AN SA NE
Mun.dauko wannan sharhin daga shafin kasar zazzzau jiya. Da yau na.facebook
#22August2023