"Shirin AGILE Alherin shi muka gani ba sharrin shi ba" Inji Gwamna Radda
- Katsina City News
- 13 Dec, 2023
- 993
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya bayyana cewa "Babu wani Aibi da Shirin AGILE Yake da shi idan ma akwai mu bamu ganshi ba Alherin muka gani" yace "Don haka Mun shirya bashi goyon baya dari bisa dari"
Gwamnan yayi wannan bayanin ne a garin Doro na Karamar hukumar Bindawa a ranar Laraba wajen Kaddamar da Shirin Raba Tallafin Fiye da Naira Biliyan 4 ga Wasu Zababbun Makarantun Sakandare 100 na jihar Katsina don gyara da gina Ajujuwa samar da kayayyakin koyarwa ga Dalibai domin habaka Ilimi a jihar.
Gwamnan yace, "Kashi Casa'in da Tara na jihar Katsina Musulmi ne, Malaman da ke koyarwa ma musulmi babu ta yanda za'ai mu gurbata kammu da 'ya'yan mu."
Yace "Shi yasa a ko da yaushe muke bawa Manyan Mutane da Malami Shawara da duk idan zasuyi magana su dunga bincike sosai don kaucewa fadin kuskure."
Radda ya kara da cewa 'A irin wannan Tunanin yasa mu Arewa a kullum muke koma baya har 'yan kudu suke mana kallon jahilai bamu san abinda muke ba, babu dalilin da zamu muhimmantar da Tallace-tallacen 'ya'yan Mata fiye da Ilimi".
Gwamnan kuma ya bayyana cewa shifa wannan Shirin na AGILE ba ma kyauta bane Bankin Duniya yake bawa Jihohi ba Rance ne kuma Duk jihar da aka bata sai ta biya.
Taron da ya gudana a garin Doro na karamar hukumar Bindawa an zabi makarantu 100 don basu Tallafin Naira Miliyan 44, 760,000 bisa kulawa da sa idon Hakimmai da masu Unguwanni don gyara Makarantu, gina Ajujuwa da samar da kayan koyo da koyarwa.
Shirin Adolescent Girls Initiative Learning and Empowerment AGILE wani shiri ne da Bankin Duniya ya samar don koyar da Mata Daliban Firamare da Sakandare (Musamman) Ilimi da basu Tallafi, kuma shirin yana Duba Jihohin Najeriya da suke da karancin karatun 'ya'ya mata da basu wuce makarantun firamare ko Sakandire suke dakatar da Karatunsu, Katsina tana daya daga cikin jihohi shida da aka zaba don gudanar da shirin a Najeriya.