An Sace Ma’aikacin Asibiti Da Dan Uwansa A Zariya
- Katsina City News
- 27 Aug, 2023
- 1185
Dama an taba kai musu hari a garinsu a can baya
Masu garkuwa da mutane sun sace wani ma’aikacin asibitin St. Luke da ke gundumar Wusasa a Zariyan Jihar Kaduna, mai suna Yusha’u da kaninsa Joshua Peter.
Da yake yi wa Aminiya karin bayani, Sarkin Wusasa, Injiniya Isiyaku Ibrahim, ya ce maharan sun afka anguwar ne da misalin karfe 9:00 na dare inda suka rika harbe-harbe kafin daga bisani su yi awon gaba da mutum biyu.
An yi ittifakin ta wannan anguwa maharan suke biyowa lokacin kai mafiya yawan hare-haren da suke kai wa wasu anguwannin birnin Zariya.
Wadanda aka sace din ’yan asalin Karamar hukumar Ikara ne da ke Jihar, kuma maharan sun taba kai hari a gidansu da ke garin inda suka sace mahaifinsu.
Duk kokarin tuntubar Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan sandan jihar, Mohammed Jalige ya ci tura, sakamakon rashin samun wayarsa a lokacin hada wannan rahoto.
Gundumar Wusasa dai ta dade tana fama da hare-haren ’yan bindiga a ’yan shekarun baya a inda ake yawan kashewa tare da dauke mutane a kai a kai.
Ita ce kuma anguwar da aka taba arangama da jami’an tsaro inda har aka kashe soja, tare da shugaban ’yan bijilan na yankin, kuma aka kona motar sojojin.
Bugu da kari, a can ne aka dauke wani Farfesa, kuma Wazirin Wusasa tare da kashe dansa wanda ya shafe kwanaki 25 a hannun mahara kafin daga bisani a sake shi, bayan biyan kudin fansa.