Ba a gina matatun mai don rage farashin fetur ba - NNPCL

top-news

Shugaban babban kamfanin mai na Najeriya NNPCL, Mele Kyari ya ce ba rage farashin man fetur ba ne babban maƙasudin gina matatun mai a ƙasar ba, sai dai ya ce wataƙila hakan ka iya faruwa.

Mele Kyari ya faɗi hakan ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin tsare-tsare da kasafin kuɗin majalisar dokokin ƙasar bisa gayyatar da majalisar ta yi masa.

Shugaban na NNPCL ya kuma ce ayyukan sabbin matatun za su inganta tare da haɓaka samar da man fetur a ƙasar cikin shekarar 2024, ta yadda ƙasar za ta zama babbar mai fitar da man fetur a shekara mai kamawa.

Ya kuma sake jaddawa cewa a yanzu kamfanin ne ke gudanar da harkokinsa ba tare da samun tallafin sisin kobo daga gwamnatin tarayya ba.

A ranar Laraba ne dai majalisar dattawan ta bai wa shugaban na NNPCL wa'adin sa'o'i 24 da ya bayyana a gabanta, yayin da a baya ya sha yin watsi da gayyatar da kwamitocin wucin-gadin majalisar ke yi masa, kan yadda kamfanin ya kashe naira tiriliyan 11 wajen gyara da kula da matatun man fetur na ƙasar tsakanin shekarar 2010 zuwa 2023.

A shekarar 2022 ne dai gwamnatin tarayya ta bai wa kamfanin cin gashin kansa, domin haɓaka tare da inganta harkokin man fetur a ƙasar.

A lokacin da yake gabatar da jawabi bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban ƙasar cikin watan Mayu, Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, lamarin da ya haifar da tashin farashin man a faɗin ƙasar.

Wani abu kuma da masana ke cewa ya janyo hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar, wadda ta fi kowacce yawan jama'a a nahiyar Afirka.

NNPC Advert