Ziyarar bazata: Dokta Tsanni ya ziyarci wasu makarantu a karamar hukumar Batagarawa
- Katsina City News
- 07 Dec, 2023
- 599
Daga Shafi'i Alolo
Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina Shawara akan Bunkasa ci gaban karkara, yakai ziyarar ba zata domin duba yadda ake gudanar da harkokin ilimi, a wasu sassa na karamar huku marsa ta Batagarawa, kamar yadda Gwamna Malam Dikko Radda ya basu umurni.
Da sanyin safiyar ranar Alhamis 07/12/2023, Mai bawa Gwamnan Shawara Dr. Abubakar Tsanni Mabudin Bargu yakai ziyarar bazatan.
A makarantar kimiyya da fasaha ta 'yan Mata dake garin Ajiwa da Makarantar sakandire ta Jeka ka dawo itama dake garin na Ajiwa da kuma makarantar firamare dake garin Shagumba.
Sauran Makarantun sun hada da Makarantar firamare dake garin Batagarawa da Kuma makarantar firamare dake garin Tsanni da kuma ta garin Yar'gamji dukkan su dake cikin karamar hukumar Batagarawa.
Ziyarar ta mai baiwa Gwamnan shawara, ta biyo bayan umarnin da Gwamnan Jihar, Malam Dikko Radda ya bada ga yan majalisar zartarwa a zaman majalisar zartarwar na ranar Laraba 06/12/2023.
Na bukatar Gwamnan abokan aikinsa kwami shinoni da masu ba shi shawara dasu taya shi sanya ido akan yadda ake gudanar da harkokin ilimi na koyo da koyarwa akananan hukumomin nasu.
A ya yin ziyarar duk da cewa zangon karantun daliban yazo karshe, ana gudanar da jarabawa, a makarantar kimiyya da fasaha ta 'yan Mata dake garin Ajiwa mai baiwa Gwamnan shawara ya nuna gamsuwar shi akan yadda shugabanin makarantar suke gudanar da harkokin koyo da koyarwa a makarantar.
Hon. Dr. Abubakar Tsanni ya zagaya a cikin wani bangare dake makarantar domin ganema idanunshi halin da makarantar take ciki tare da duba yadda daliban suke gudanar da harkokin su.
A makarantar sakandire Jeka ka dawo dake garin na Ajiwa kuwa, Mai baiwa Gwamnan shawara anan ma ya zagaya domin duba halin da malamai da daliban suke ciki duk da zangon karantun yazo karshe Suma, amma duk da haka Malaman su na iya kokarinsu na ciyar da ilmin gaba.
Ya kuma yaba, tare da godema malaman makarantar akan yadda suke gudanar da aikin su tare da basu tabbacin cewa" Zai sa ke dawo wa, idan an dawo hutu domin sa ke kawo irin wannan ziyarar ta bazata domin ganin yadda ake gudanar da harkokin koyar da ilmin.
Dr. Tsanni Soja ya nuna rashin jin dadinsa a makarantar firamare dake garin Shagumba, da ta garin Alale da kuma ta garin Kaukai akan yadda daliban basu fahimtar abinda ake koya masu, ya Kuma ja hankalin malaman dasu kara dagewa wajen sauke nauyi da aka dora masu.
Daga karshe bayan kammala ziyarar tasa zai kammala bayanansa na abinda ya ganema idanunsa domin kaima Gwamna Malam Dikko Umar Radda kamar yanda ya umurta suyi.
Wanda ya bayyana wannan ziyarar tasu, ba karamin Farfado da harkokin Ilimi zatayi ba, a Jihar Katsina Karkashin Gwamna Radda, Duba da duk abinda su ka gani na gyara ko na yabo zasu fada mashi tsakaninsu da Allah SWT.