TARIHIN YANDA SARAUTAR YARIMA TA SAMO ASALI A MASARAUTAR KATSINA:
- Katsina City News
- 07 Dec, 2023
- 1348
A nan Katsina sarautar Yarima sarautace ta Dan Sarki Mai jiran gadon sarauta, ta samo asali ne sakamakon bukatar wanda zai wakilci sarki idan bayanan ko bashi da lafiya, da kuma dangane da abubuwa da suka shafi sha'anin na sarauta.
Yarima shine Shugaban Ya'yan sarakuna a lokacin Mulkin Dallazawa, mafi a kasari yawanci anfi ba Babban Dan sarki Mai jiran gadon sarautar Mahaifinsa.
Ita wannan sarauta ta Yarima Daular Fulani suka aro ta daga Daular Barebari ta kasar Borno koda yake tarihi ya nuna kusan duk Inda ake Mulki cikin duniya Yarima shine wanda yake Zama dan sarki Mai jiran gadon sarauta.
A nan Katsina ma haka abin yake a cikin karni na goma Sha hudu sarkin Katsina Muhammadu Korau ya nada dansa Mai suna Usman Maje wajejen shekara ta 1348, daga nan wannan sarauta ta cigaba har zuwa lokacin da jihadin Shehu Usman Danfodiyo yazo na jaddada addinin musulunci Karkashin jagorancin Malam Umarun Dallaje a Katsina.
Bayan an kammala jihadi fulani sunyi nasara sai Malam Umarun Dallaje ya Zama sarkin Katsina, a dai dai wannan Lokacin ne Malam Umarun Dallaje ya nada Babban dansa Muhammadu Bello sarautar Yarima da sauran wasu sarautu na cikin gida dana waje.
Wannan ya nuna sarautar Yarima ta dan sarki ce Mai jiran gadon sarauta idan bukatar hakan ta taso gami da kaddarawar Ubangiji ga yanda yaso.
Haka kuma sarautar Yarima sarautace wacce ba tada ta gaba gareta domin tarihi ya nuna itama sarakunan karaga ke zaben ta kamar yanda ake zaben sarki.
Sannan lokacin nadin sarautar Yarima a kan bashi kayan sarauta kamar irin su Alqur'ani takalma, rawani, takobi, dawaki, barori da bayi domin yi Masa hidima, haka idan angama nada yarima a kan buga Masa tambari na sarauta, sa'annan sarki yayi Mashi addu'a ta fatan Alhairi.
Daga lokacin da aka nada Yarima yanada ikon hukunta duk wani Mai laifi idan ya aikata abinda ba dai dai ba, haka yanada ikon yankan haraji kuma yanada ikon nada wanda yakeso sarauta.
A lokacin Mulkin Dallazawa duk karshen mako Yayan sarakunan Dallazawa din sukan taru gidan Yarima dake sansanin yan sarki cikin birnin Katsina domin suje su gaida sarki, haka bayan an dawo daga wannan gaisuwa ana rako Yarima gida sannan ayi ban kwana daga nan kowa zai tafi nasa gidan, wannan yana nuni da cewa Yarima shine wanda ake kyautata zaton shine wanda zai gaji sarautar Mahaifinsa.
Tarihi ya nuna wayanan kayan sarauta da ake nada Yarima dasu kayane da Sarkin Katsina Mal Umarun Dallaje Yayi yakin jihadi dasu, sune lokacin daya nada Babban dansa sarautar Yarima ya dauko su ya bashi a matsayin kayan sarauta duk wani Yarima da aka nada a lokacin Mulkin sarakunan Dallazawa da sune aka nada shi dasu.
1. *ALKUR'ANI* - Shine wanda Mal Umarun Dallaje ya rinka yawon wa'azi dashi.
2. *RAWANI* Shine wanda Mal Umarun Dallaje ya ke nadawa a kansa idan za shi masallaci ko wajen yakin jihadi.
3. *TAKOBI* ita ce wadda Mal Umarun Dallaje ya rinka amfani da ita lokacin jihadi.
4. *TAKALMI* su kuma wayannan takalma suma na Mal Umarun Dallaje ne da yake amfani dasu.
5. *WUNDI* itama wata tabarma ce da sarakuna ke amfani da ita lokacin da.
Kana sai a hada shi da Dawakai da bayi da Barori a raka shi gida.
Duka wayannan abubuwan da ake nada yarima lokacin da Dallazawa ke sarauta yanzu babu su, yanzu ana nada yarima kamar yanda ake nada kowane hakimi.
YANDA SARAUTAR YARIMA TA KASANCE LOKACIN MULKIN FULANI DALLAZAWA:
1. Bayan da jihadi ya kare sarkin Katsina Mal Umarun Dallaje ya Zama shine Shugaba shine Limami shine Alkali shine sarki Mai cikakken iko.
A shekara ta 1808 an zauna an tsara yanda za'a rinka tafiyar da Mulki yanda shari'a ta yarda da ayi, an gina Babban masallacin juma'a da makarantu na kowon addinin musulunci da kafa baitul mali, sai aka Fara nade nade na wayanda zasu rinka taimakama Amir Mal Umarun Dallaje wajen sha'anin gudanar da Mulki.
Cikin nade naden da Yayi ya nada Babban dansa Muhammadu Bello sarautar Yarima a shekara ta 1809-1836, Inda daga baya a kayi Masa Murabus bisa wannan sarauta.
2. Bayan rasuwar Amir Mal Umarun Dallaje sai Allah ya kaddara dansa Abubakar Saddiku wanda yake sarautar Durbi ta kasar Mani ya Zama sarki, lokacin da ya hau sarauta sai ya dauko dan uwansa Muhammadu Jabba ya bashi sarautar Yarima, shi kou lokacin yana sarautar Dan Yusufa a kasar Bindawa.
Ana cikin wannan hali cikin hukuncin Ubangiji sai Allah ya kaddara sarki Abubakar Saddiku ya samu rashin Fahimta tsakaninsa da sarkin musulmi Aliyu Babba ya cire shi daga sarauta.
3. Bayan cire Abubakar Saddiku daga sarauta sai Allah yaba Muhammadu Bello sarautar Katsina Babban Dan Amir Mal Umarun Dallaje kenan, wanda sarki saddiku din ya yima Murabus yana Yarima.
Shima sarki Muhammadu Bello lokacin da hau sarautar Katsina sai ya canza Muhammadu Jabba daga sarautar Yarima din ya nada shi sarautar Binoni wacce itama sarautace ta Yayan sarakunan Katsina tun daga Habe har zuwa Dallazawa.
Bayan ya canza Mashi ita sai ya sarki Muhammadu Bello ya nada dansa Ibrahim sarautar Yarima a shekara ta 1845-1869.
4. Bayan rasuwar Sarkin Katsina Muhammadu Bello sai Allah yaba Ahmadu Garnakaki sarautar Katsina.
Sarki Ahmadu Garnakaki shima dan Mal Umarun Dallaje ne, amma shi a lokacin sabani yaso ya auku tsakaninsa da dan uwansa, saboda dukansu Yayan Mal Umarun Dallaje ne kuma sunansu iri daya, amma kowa yanada nashi lakanin da ake kiransa domin banbamcewa.
Ahmadu Garnakaki shine wanda ya ke sarautar Kankiya.
Ahmadu Dan kyau kuma shine yake sarautar Bindawaa matsayin Dan Yusufa kuma dukansu sun fito neman sarautar Katsina.
Lokacin da sarkin musulmi ya aiko Galadiman Sakkwato da takardar zaben sabon sarki, lokacin da yake cikin karanta takardar sai Ahmadu Garnakaki yaji an ambaci Ahmadu bai bari an karisa ba sai yayi zumbur ya tashi yace shine wanda sarkin musulmi yake nufi, abin yaso ya tayar da hayaniya har shi Ahmadu Garnakaki ya zare takobi da nufin cewa duk wanda yayi jayayya zai dau matakin kawar dashi.
Dama kuma yazo da wasu baradensa wayanda ake Kira da Gwarawa ko a fagen yaki tsoronsu ake idan suka fito.
Allah Mai iko cikin hikimarsa yasa dan uwan nasa ya Mike ya Fadi yayi mubaya'a gareshi yace na bika kai Allah ya zaba baiyi jayayya ba.
Wannan yasa lokacin da Ahmadu Garnakaki ya shiga gidan sarauta sai ya dauko Babban dan Ahmadu Dan kyau ya bashi sarautar Yarima a shekara ta 1869-1870, shine Yarima Ahmadu Maigida, a na Masa lakabi da Maigida ne saboda sunan Mahaifinsa ne kuma shine Babba a gidan nasu.
Shi kuma yarima Ibrahim aka maida shi kandawa yayi Murabus.
Sai dai kuma Allah Mai iko yanda yaso sarki Ahmadu Garnakaki baiyi tsawon kwanaki bisa gadon sarautar Katsina ba Allah ya amshi rayuwarsa.
5. Bayan rasuwar Sarkin Katsina Ahmadu Garnakaki, cikin kaddarawar Ubangiji da yake bada Mulki ga wanda yaso lokacin da yaga dama, yaba Ibrahim sarautar Katsina.
Shima sarkin Katsina Ibrahim lokacin da ya hau kan gadon sarauta sai ya canza Yarima Ahmadu Maigida daga Yarima ya maida shi Kankiya, ita kuma sarautar Yarima ya nada dansa Abubakar a shekara ta 1870-1882, lokacin daya rasu.
6. Bayan rasuwar sarkin Katsina Ibrahim sai Allah yaba Mal Musa sarautar Katsina, shi ko Mal Musa dan Amir Mal Umarun Dallaje ne.
Lokacin da hau sarauta sai ya yima Abubakar Murabus daga sarautar Yarima amma shi ba'a canza Mashi wani guri ba kamar yanda saura su kayi.
Sarkin Katsina Mal Musa ya nada jikansa sarautar Yarima a shekara ta 1882-1887, shine Yarima Ahmadu.
7. Lallai Mulki na Allah ne yau Abubakar ya Zama sarkin Katsina wanda shima a kayiwa Murabus daga sarautar Yarima.
Lokacin da Sarkin Katsina Mal Musa ya rasu mutane da Dama sun fito neman sarautar Katsina daga gidan na Dallazawa.
Amma cikin hukuncin Ubangiji wayanda suka fito neman wannan sarauta sai Allah sai ya kaddara cewa Sarkin Musulmi Umaru dan sarkin Musulmi Aliyu Babba ya aiko da takardar tabbatar da Sarki Abubakar sarauta.
Wasu daga cikin masu takarar neman sarautar Katsina a lokacin sun alakanta zaben Abubakar sarautar Katsina da sarkin musulmi yayi yanada nasaba da alakar da take tsakanin gidan Sarkin Musulmi Abubakar Attiku II da Sarkin Katsina Ibrahim mahaifin Sarki Abubakar din.
Wanda suke ganin mahaifin sarki Abubakar din ya auri diyar sarkin musulmi Abubakar Attiku na ll.
Haka ko bayan rasuwar sarki Ibrahim din jikokin nasu sun kasance hannun Abubakar har zuwa lokacin daya Zama sarkin Katsina.
Shima sarkin Katsina Abubakar bayan ya Zama sarki sai ya yima Yarima Ahmadu Murabus ya nada dansa Abdulkadir sarautar Yarima 1887-1905.
8. Yero ya Zama sarkin Katsina.
Bayan da turawan Mulkin Mallaka suka shigo kasar Hausa suka cire sarki Abubakar daga sarauta saboda yaki yarda da suyi amana, sai aka dauko Mal Yero a ka bashi sarautar Katsina.
Shi kuwa Mal Yero lokacin Sarki Abubakar din ya cire shi daga sarautar Durbi, ya koma tsanni ya zauna, lokacin da ya samu labarin abinda ya samu Abubakar sai ya fito neman sarautar Katsina, kuma Allah ya bashi,
Shima da hawansa sai ya yima Yarima Abdulkadir Chanjin sarauta ya maida shi Kankiya.
Ana cikin wannan hali sai shima sarki Yero aka kulla Mashi makirci kamar yanda aka yima dan uwansa Abubakar a ka cire shi daga sarauta, bai kai ga nada wani sabon Yarima ba.
A cikin shekarar 1910 baturen ingila yazo Katsina yana tambaya ina Yarima Abdu yake aka fada Masa ai Yarima Abdulkadir yanzu bai rike da wata sarauta yana can daji zaune suna noma abincin da zasu ci dashi da yan'uwansa, wannan dalilin yasa baturen ya bukaci ganin yarima Abdu.
Daga karshe an yanke shawarar bama yarima Abdulkadir kasa da zaije ya zauna da jama'arsa.
Wannan abu da a kai ba kowa yayi wa dadi ba harda shi kansa sarki Muhammadu Dikko din, sai ko tsiraru daga cikin Masarautar ta Katsina, sai dai ba yanda zaayi dole a kayi abinda baturen nan keso.
A Lokacin duk hakimin da aka ce za'a kai Yarima Abdulkadir kasarsa sai yaji tsoro, saboda an rinka tsoratar da hakimai cewa idan suka sake Yarima Abdu ya zauna kasarsu zai cinye garin saboda Dan sarki ne.
Wannan bai hana yandaka Mani yarda da azo kasarsa a sararma Yarima Abdulkadir kasa domin yazo ya zauna ba.
Lokacin da Dikko yaji labarin haka yasa dole ya yarda aka yankama Yarima Abdulkadir Tsaskiya a matsayin mai sarautar gurin, wannan ya nuna Yarima Abdulkadir shine wanda ya riki sarautar Yarima har sau biyu tun lokacin da Mahaifinsa Sarki Abubakar ya nada shi Yarima ba wanda aka sake nadawa har ya rasu a shekara ta 1971.
Koda yake a shekara ta 1905 bayan sarki Mal Yero ya yima Yarima Abdulkadir canjin sarauta ya maida shi Kankiya, ana cikin wannan hali sai turawa suka cire Mal Yero daga sarautar Katsina, a cikin shekarar 1906 Durbi Dikko yana rikon kwarya kafin ayi tunanin wanda zai Zama sarki daga gidan na Dallazawa, amma abin yaci tura an kulla makirci kuma yayi tasiri ga turawa.
Daga karshe turawan Mulkin Mallaka sun tabbatar ma da Durbi Dikko da sarautar Katsina a shekara ta 1907, bayan Dikko ya Zama sarki ya cire Yarima Abdulkadir daga sarautar Kankiya da Sarki Yero ya kaishi ya nada kanensa Kankiya Nuhu wannan sarauta, wannan dalilin ne yasa yarima Abdu ya koma gonarsu ta gado da suke nomawa a kauyen tarkama kasar kaita.
Haka Dikko din ya dauko wani Mai suna Yaro wanda a kace dan aminin Mahaifin Dikko ne a ka bashi sarautar Musawa a matsayin Yarima, wannan abu bai yiwuba domin ko Yarima Abdulkadir yaki yarda da abinda Dikko yayi, saboda ya sabama yanda a kayi alkawari cewa ba wanda za'a nada sarautar Yarima in banda Badallaje.
Abubuwa sunyi gauri da yawa domin sai da a kayi kamar taho mugama da Yarima Abdulkadir da Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, daga karshe an dai dai ta an barma Dallazawa wannan sarauta ta Yarima.
Shi kuma Yaro a ka maida sunan sarautar shi sarkin Musawa, kuma daga wannan Lokacin ne sarautar Musawa ta tashi daga sunan Yarima ta koma ta sarkin Musawa.
Wannan ya nuna Yarima Abdulkadir shine wanda ya jajirce wajen tabbatar da tsayuwar wannan sarauta ta Yarima a gidan na Dallazawa,
an kuma nada shi 1887-1971.
Ga yanda jerin sunayen nasu yake:
1. Amir Katsina Mal Umarun Dallaje
Yarima Muhammadu Bello ( 1809-1836 )
2. Sarkin Katsina Abubakar Saddiku
Yarima Muhammadu Jabba ( 1836-1845 )
3. Sarkin Katsina Muhammadu Bello
Yarima Ibrahim ( 1845-1869 )
4. Sarkin Katsina Ahmadu Garnakaki
Yarima Ahmadu Maigida (1869-1870 )
5. Sarkin Katsina Ibrahim
Yarima Abubakar (1870-1882 )
6. Sarkin Katsina Mal Musa
Yarima Ahmadu ( 1882-1887 )
7. Sarkin Katsina Abubakar
Yarima Abdulkadir ( 1887-1971 )
8. Sarkin Katsina Mal Yero
Bai nada Yarima ba
Dukkan wayanda su kayi sarautar Yarima daga 1809-1906 a musawa ne suka yi wannan sarauta, sai a shekara ta 1910 sarautar Yarima ta koma Tsaskiya/Safana har zuwa yau.
Masu rike da wannan sarauta har yanzu Dallazawa ne iyalin Sarkin Katsina Malam Umarun Dallaje.
Kada mai karatu yaga yanda sarautar Yarima ta rinka canza kanta daga wannan gida zuwa wancan gida, amma duka a cikin gidajen sarautar Dallazawa din, haka sarautar Yayan sarki ta gada duk wanda yake sarauta yawancin Babban da shine wanda ake nadawa sarautar Yarima, wannan ba wani abu bane sabo haka abin yake kusan ko'ina.
Bayan Yarima Abdulkadir ya rasu an nada dansa Yarima Ahmadu Rufa'i a shekara ta 1971-1990.
Shima bayan ya rasu aka nada dansa Yarima Sada Rufa'i 1991- har zuwa yanzu shine yake sarautar Yarima.
KATSINA GIDAN DALLAJE, TA MALAM UMARU MA DAUKIN TUTA.
Daga Musa Gambo kofar soro.
Musa mai shaawar binciken tarihi ne, daga zuriyar badawan Katsina, kuma ma aikacin gwamnatin Tarayya yana zaune da iyalan shi a Katsina