Kasafin 2024 ya bada fifiko ne wajen jaddada Ajandar Saisaita Nijeriya - Idris
- Katsina City News
- 05 Dec, 2023
- 632
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Kasafin Kuɗi na shekarar 2024 ya nuna lallai an fara taka tsanin samun nasarorin ƙudirorin sake bunƙasa ƙasa a ƙarƙashin Ajandar Saisaita Nijeriya ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ministan ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Kaduna, yayin da ya ke jawabi a taron shekara wanda Cibiyar Faɗakar Da Jama'a ta Nijeriya (NIPR), reshen Jihar Kaduna, ta shirya.
Ya ce baki ɗayan kasafin 2024 an bijiro da shi ne bisa zurfafa nazarin manya da ƙananan ƙalubalen da ke fuskantar ƙasar nan, don haka ne aka tsara kasafin yadda zai fara da zaburar da hanyoyin bunƙasa ƙasa da kawo cigaba mai ɗorewa, inganta tattalin da kuma wanzar da yalwar arziki a ƙasa baki ɗaya.
Ya ce: "A cikin wannan satin ne Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da Kasafin Kuɗi na 2024 na naira tiriliyan 27.5 ga Majalisar Tarayya, wanda shi ne kasafin sa na farko tun da ya kama mulkin sa. Kasafin kamar yadda ya gabatar da shi, bigire ne na fara taka tsanin tabbatar da cin nasarar Ajandar Saisaita Nijeriya, ta hanyar bada fifiko ga ƙudirorin gina ingantaccen tattalin arziki.
"Sannan kuma kasafin ya nuna yadda gwamnatin Tinubu ke taka-tsantsan da tsantseni wajen bada fifikon kashe kuɗaɗe a hanyoyin da su ka dace, domin ta hakan ake gina ginshiƙin tsarin tattalin arziki mai nisan zango.
"Yayin da Kasafin Kuɗi na 2024 ya tafi hannun majalisa domin yin nazari da tsettsefe shi, mu na da kyakkyawan yaƙinin cewa kasafin zai kasance matakin farko na bin turbar saisaita Nijeriya, kawo cigaba da inganta rayuwar 'yan Nijeriya."
Haka kuma Ministan ya ce kafin Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin, sai da ya yi ƙwarya-ƙwaryan kasafi, ya sa wa ƙudirori hannu sun zama doka, kuma ya kafa kwamitin shugaban ƙasa kan tsare-tsaren kuɗaɗe da tattalin arziki, kwamitin iskar gas (CNG), Shirin Bunƙasa Abinci, Shirin Tallafa wa Matsakaita da Ƙananan Masana'antu (MSME) da sauran fannoni masu muhimmanci wajen raya tattalin arziki.
Ya ce: "Muradin da ake so a cimma shi ne samar wa ɗan Nijeriya rayuwa cikin sauƙi, tare da gina tushen dawwamammen yalwar arziki."
Ya ce tilas fa sai 'yan Nijeriya sun bai wa wannan gwamnati uzirin cewa ta kama mulki a wani mawuyacin hali ne, amma kuma duk da haka shi Shugaban Ƙasa ya tarbi gaban kowane ƙalubalen da ake tunkara ko ya ke tunkaro ƙasar nan.
Ya ce, "'Yan Nijeriya sun yi katarin samun shugaba wanda ke da ƙwarewa sosai a ɓangaren harkokin hadahadar tattalin arziki da kuma gogewa a gwamnatin jiha.
"Shugaba Tinubu ba mutum ne da zai yi ko gezau ba yayin da duk wani ƙalubale ya tunkare shi. Kuma da kan sa ya ce ba ya buƙatar a tausaya masa, domin shi ya nemi a ba shi shugabanci, saboda ya san zai iya."