WAIWAYE DA TUNAWA DA MARIGAYI ADAMU YUSUF BBC
- Katsina City News
- 01 Dec, 2023
- 950
Daga Aliyu I. Kankara, Katsina Times
A duk lokacin da na tuna da marigayi Alhaji Adamu Yusuf, tsohon wakilin tashar radiyon BBC da ke London sai in ji kamar in fashe da kuka. Sai in xaga kai na sama in ga sararin samaniya ta yi ma ni baqi-qirin, jikina ya shiga rawa kamar mazari sabili da kixima. Ba sai na bayyana ma Duniya Adamu mai kyauta, alheri, son jama’a da rashin wulaqantasu ba ne. Cike gurbinsa na da matuqar wahala. Wannan, wata babbar sa’a ce daga Ubangiji. Saidai, kwaram sai Allah Ya kawo ajalinsa ran 1/8/2007, wanda ya jefa duk na tare da shi cikin maraici, baqin ciki da shiga halin ‘ni ‘ya su’. Babban halin Adamu BBC shi ne kyauta, nuna jin qai, samar wa mutane sana’a ko aikin yi da kuma neman zaman lafiya da kowa. Adamu, ya yi tarayya da kowa, ya taimaka ma kowa, ba tare da ya na duba wanene kai, ko daga ina ka fito ba. Bayan ma waxannan halaye, akwai sauran halaye na qwarai da aka san Adamu da su, na kyautata ma maqwabta da makarantu da bayar da gudunmuwa ga ayyukan da za su kawo ci-gaba ga al’umma daban-daban. Jama’a, ma’aikata da ‘yan kasuwa da ma su galihu da ma marasa galihu kan taru a gidansa a ko da yaushe, a ci abinci, a sha, a tattauna akan muhimman abubuwan rayuwa. Sannan, wani babban hali na Adamu shi ne damar da ya samu na amso kujerun Makka ya na bai wa waxanda ya yi tarayya da su, ko Umara, a duk shekara. Misali: a shekarar 2004 mu 16 Alhaji Adamu ya kai Saudiyya mu ka sauke farali. Toh, duk shekara haka ya ke yi, Makka da Umara. Ya kan yi hanya akai mutum Makka, yak an amso kujeru daga gwamnatin Tarayya da ta jihar Kaduna, ya kai kuma kai mutane da kuxin aljihunsa. Wannan ya daxa sanyawa ya qara samun masoya da ma su zuwa wajensa don su yi mu’amulla. Wannan ya sanya aka rinqa kallonsa kamar wani xan qaramin ‘Sardauna’. Wasu ‘yan siyasa da dama da su ka samu nasarar lashe zave a mahaifarsu sun samu taimakon Adamu na haxa su da wasu iyayen gida a siyasar. To hakama ‘yan kasuwa, Adamu ya sada su da wasu muhimman mutane a Arewa don havaka kasuwancinsu. Jiddadin, aikin ke nan. Kullum ba ya rabo da jama’a ma su neman taimako, domin shi babban tsani ne. Kai, a dai gajarce labari, da Firimiya Ahmadu Bello Sokoto da Adamu Yusuf BBC sun haxa wasu halayya tare, na a ko da yaushe gidajensu a buxe su ke a Kaduna, kowa na iya shiga ya yi hira, ya ci abinci, ya huta. Kowannensu na da tsananin kishi da qaunar talaka. Ba zan manta ba, na fara ganin da sanin marigayi Adamu BBC a xakin taro na Gidan Arewa lokacin da Dokta Adamu Ibrahim Malumfashi na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ya qaddamar da wata jarida da ya fara wallafawa, sa’ilin ya na yin aiki na wucin-gadi a Kamfanin jaridar Gaskiya Tafi Kwabo, cikin 1996. A wajen taron, jawabin da na yi ya ja hankalin Adamu matuqa amma ba mu haxu mu ka zanta ba. To kuma sai cikin 1997 lokacin da na fara aiki a Kwalejin Ilimi mai zurfi ta Kaduna, wani matashi kuma sabon marubuci ya nemi in haxa shi da Adamu xin, nay i karambanin kai shi wajensa. Wannan shi ne karo na farko da na fara zuwa gidansa a bakin ruwa, Kaduna. Bayan tattaunawa akan gabatar da wannan matashi sai Adamu ya buqaci da in rinqa zuwa gidansa domin yin hira don a rinqa saduwa da jama’a saboda a gaba. A taqaice, na fahimci Adamu mai son jama’a ne ballantana da ya ji na ce ma sa ina koyarwa a Kwalejin Ilimi mai zurfi ta Kaduna. Nan take na aminta. Don haka na ci-gaba da halartar gidan Adamu, ana hira, ana haxuwa da jama’a iri-iri, ma su ayyuka da sana’o’I kala-kala. Wannan ya ba mu dama mu ka zama tamkar ‘yan uwa, ni da Adamu da kuma sauran jama’arsa. A duk lokacin sallah babba ko qarama, Adamu za ya kawo kayan sallah da nama ya raba ma duk wani xan qungiyarsa. Idan ma ba ka nan to za ka ga aike har gidanka. Sannan, lokacin da ba sallah ko azumi ba, wuci-wuci, Adamu kan aika ma na da hasti na abinci ko sutura gidajenmu. Wata babbar nasara ga rayuwar Adamu BBC ita ce da ya yi tarayya da manyan mutane a Arewacin Nijeriya ta dalilin aikinsa na New Nigerian da Gaskiya Tafi Kwabo da kuma daga bisani BBC xin, waxanda, mu kanmu, mu ka samu damar yin mu’amulla da wasunsu, kamar su: Saifullahi Muntaka Kumasi, Alhaji Sule Kofar Sauri, Ahmed Mohammed Makarfi tsohon gwamnan Kaduna), Bilkisu Yusuf (‘yar jarida da ta rasu a Makka), Hajiya Laila Dogonyaro, Kanar Bala Mande (tsohon gwamna kuma tsohon Ministan Muhalli), Farfesa Ladi Sandra Adamu Pankshin Ahmadu Bello, Zariya), da sauransu. Ta dalilin Adamu, mun san wasu ma’aikata da wakilan tashar Radiyon Amurka da na London waxanda kan je gidan sa su yi masauki, kamar su Ahmed Abba Abdullahi, Abba Mohammed Katsina, Jamila Tangaza, Abubakar Kabir Matazu, Sani Abdullahi Tsafe (Xanmasanin Tsafe) da sauransu. Ban tava ganin Halima Jimrau ba amma Adamu ya haxa ni da ita ta wayar tarho mun gaisa, da dai wasu da dama da farat da garaje ba zan iya tuna sunayensu ba. Mutane da dama sun nemi taimakon Asdamu domin samun wasu abubuwa na rayuwa da su ke nema, ba ma dai waxanda ke so a haxa su da Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Alhaji Ahmadu Cancangi, Janar Ali Gusau, Alhaji Shehu Shagari da sauransu. Hatta Janar Sani Abacha ya san Adamu sarai. Sannan, Adamu ya i hulxa ko tarayya da manyan malaman addinin musulunci kamar su: Malam Bawa mai shinkafa, Malam Xan Gungu, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun, Sheikh Mohammed Tureta, da sauransu. Alhaji Ahmadu Chanchangi da Alhaji Garba Xanshagamu sun zama ma kamar abokai da Adamu, don su na tare da shi a ko da yaushe. Cikin Afrilun 1999 na tafi Funtuwa wajen Dokta Mamman Shata, na ga ya na kwance, bayan ya dawo daga Jidda, sai naje na shaida ma Adamu, da na koma Kaduna. Wanshekare Adamu ya shirya ya tafi Funtuwa ya gana da mawaqin, shi da manyan aminansa kuma maqwabtansa, Alhaji Kabiru Uba da Alhaji Labaran Yawuri. Wannan ita ce ganawarar Shata ta qarshe da ‘yan jarida a Duniya, jim kaxan kafin rasuwarsa, domin sun yi hirar da shi ran 27/4/1999. Ni na assasa wannan ziyara da hira. A cikin littafina na tarihin Adamu Yusuf BBC da na raxa ma suna Zakaran Gwajin Dafi: Tarhin Adamu Yusuf BBC, na bayar da bayanin asali (daga Nupe) da yanda mahaifinsa, Alhaji Yusuf ya zo Kaduna daga Wushishi cikin 1932. Na kuma yi tsokaci akan haihuwa da yarintar Adamu (an haife shi ran 6/6/1961) da shigarsa makaranta da wata rashin lafiya da ta same shi wadda ta kawo ma sa givi a karatunsa, da warkewarsa. A lokacin haxa littafin ne kuma na samu damar zuwa ina yin hira da mahaifiyar ta sa, Hajiya Habiba, wata Banupa, dattijuwa mai haquri, mai sanyin zuciya, mai kawaici (Allah Ya gafarta ma ta) Ganin qwazo na da dagewata akan littafin Shata da na yi ya sanya Adamu ya ba ni dama in wallafa na sa littafin shi ma. Ina ma iya tunawa cewa a ran Litinin, 8/6/1998 da asuba na ziyarci Adamu a gida, mu ka zauna a ofishinsa da ke cikin gidansa, na fara yin intabiyu da shi akan littafin na sa, a ranar ne kuma, a kuma daidai wannan lokacin ne ma Shugaban Qasar Nijeriya, Janar Sani Abacha ya rasu. Abin da ya ba ni al’ajabi, ba mu ji labarin rasuwar Abacha ba sai da marece, amma yaya aka yi, Adamu ya na wakilin BBC bai samu labari ba lokacin da abin ke, ko ya faru? Mu na nan dai tare da Adamu ban ji wani daga Abuja ko Kaduna ya bugo ma sa waya ba ballantana in yi zaton ko an faxa ma sa labarin rasuwar, shi ya qi faxa ma ni ne. Har ila yau, a cikin littafin, na yi batu akan Mista Godwin Kadzgi, qaramin jakadan Qasar Jamus a Nijeriya wanda ke da ofis a Kaduna. Shi ma, ya saba da Adamu matuqa, a tsakanin 1983 da 1985. Domin jin daxin tarayyarsu, da Mista Godwin ya koma qasarsu sai ya nemi gwamnatinsu ta bas hi gurbin zuwan Adamu da abokinsa ziyara can, aka kuma yi haka. Jamus ta gayyaci Adamu da abokinsa su ka tafi can ziyara na sati biyuLittafin kuma ya yi bayani mai kauri akan yanda Adamu ya fara aiki da Kamfanin Jaridar New Nigerian a cikin 1978 da yanda ya fara yin karambanin zuwa sashen Gaskiya Tafi Kwabo ya na yi ma su rubutu sun a wallafawa. Na kuma yi bayanin tarayyarsa da marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi. Mu na iya cewa abokin Adamu ne, Ado Saleh Kankiya da ya tafi aiki da BBC London ya ja hankalin Adamu har ya fara yi ma su aiki a matsayin wakilinsu. Amma sai da Sheikh Gumi ya sanya baki sannan ya amince don a lokacin ya na aiki. Har ila yau, a cikin littafin, na bayyana irin tarayyarsu da Janar IBB da ta yi kauri har ta sanya shi, IBB xin ya sa Adamu ya zamana cikin ‘yan jaridar da gwamnatin Tarayya ta tura fidda iyakar Nijeriya da jamhuriyar Benin cikin 1987. Adamu na cikin tawagar ‘yan Nijeriya da su ka kai ziyara Jihar Jojiya ta Qasar Amurka cikin 1996. Babban abin da ya bambanta Adamu da sauran mutane ma su hali, kamar yanda na ambata shi ne yawan kyauta da kasancewarsa mutum mai sauqin kai, sannan, na tare da shi sun ji daxi qwarai da gaske don ya yi ma su hidima. Ko da yaushe gidansa na cike da mutane, a zauna a ci, a sha, a tattauna akan al’amurran rayuwa tare da neman ma su mafita ma. Toh, a yau, zai mu aza cewa ya na da wuya a samu irinsa a cikin jama’a ma su hali da dama, kamar dai ka ce ka na neman ruwa ne a tsakiyar Sahara. Kamar yanda a lokacin Adamu, ake ta yawan tattaunawa, har yau, Arewa ta rasa magabata da za su kare ta dangas. Yau, mu na ji mu na gani, qasashen qetare sun kutso sun kawo mana Boko Haram da ta’addanci a Arewa, sun wargaza mu, sun wargaza ma na tattaklin arziki, sun kore mu daga mahallanmu da gonakinmu, su kama matansu su yi fasiqanci da su, mu kuma tafi mu biya kuxin fansa mu amso su. A yau, fulani, jahilai, ‘yan ta’adda sun mallake ma na gonakinmu, su na ta kasha mu, gwamnati kuma ta na ji ta na gani ta sanya ma sun a mujiya. Irin faxan da Adamu kan yi na rashin kishin Arewa, to a yau, babu ransa amma abin ya qara ta’azzara. Qiri-qiri manoma a Arewa sun koma hedikwata ta qananan hukumomi sun zama mabarata, sun talauce. Wanda ake tunanin za ya zo mulkin Nijeriya ya yi ma Arewa maganin matsalolinta, Janar Muhammadu Buhari, to da ya zo sai ma ya qara hasa bala’I da tashin hankali. Kusan, babu abin da mulkinsa ya tsinana sai kawo koma baya da rugujewar tattalin arzikin Qasa, abin da Adamu ya yi ta kumfar baki kada ya faru a Arewa a shekarun baya. A yau, mu, mutanen Adamu Yusuf BBC, a yanda mu ka san halinsa da kishinsa na Qasa, watau horonsa, mun fi kowa ganin tashin hankali da takaici na daga abubuwan da ke afkuwa a Nijeriya. Aliyu I. Kankara ya rubuto daga birnin Katsina,07030797630/ialiyu260@gmail.com