Tsohon Gwamnan jihar Katsina ya samu Kyautar girma daga Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua
- Katsina City News
- 24 Nov, 2023
- 658
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
"Tsohon Gwamnan jihar Katsina Barasta Ibrahim Shema, Mutumin da ya Sadaukar da Rayuwarsa don Al'umma" -Dikko Radda
Dokta Ibrahim Shehu Shema Nagartaccen Mutum ne kuma jagora na gari, inji Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda da ya samu wakilcin Mataimakinsa Hon. Faroq Lawal Jobe a wajen taron Karrama tsohon Gwamnan da Makarantar koyon Ilimin Shari'a (Faculty of Law) a Jami'ar Umar Musa 'Yar'adua ta shirya babban dakin taro na Auditorium.
Gwamnan yace "Babu shakka Dokta Shema ya mulki jihar Katsina a cikin wani salo na kwarewa da sanin Makamar aiki a shekarar 2007 zuwa 2015."
Yace "Gwamnan ya bada gudummawarsa dari bisa dari wajen haba jihar Katsina musamman Ilimi da Matasa".
A nasa jawabin jim kadan bayan karramawar tsohon Gwamnan jihar Katsina Barasta Dokta Ibrahim Shehu Shema ya bayyana godiya bisa wannan Karrama, sana ya yaba da salon mulkin Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda, wanda ya e ya fara da salon mulki na kwarewa, ya kuma biyo Hanyar kai jihar ga Tudun mun tsira.
Daga karshe, Barista Ibrahim Shema, wanda ya bayyana jihar Katsina a matsayin cibiyar ilimi ta arewacin Najeriya, ya kuma bukaci al'umma da su cigaba da yi ma shugabanni addu'a wadanda ke mulki yanzu da ma wadanda suka shude.
Tun da farko, Dr. Sirajo, HOD na International Law, Nile University a Jami'ar Abuja ya gabatar da Mukala akan Asalin jihar Katsina jihar Ilimi.
Sauran wadanda sukai jawabai a wajen taron sun hada da Dokta Binta Dalhat Danladi, Dean Faculty a sashin shari'a, Farfesa Shehi Salihu Muhammad, Farfesa Muhammad Arsalan Muhammad na sashin Shari'ar Muslunci a jami'ar ABU, Farfesa Abdulrazaq na Allah daga Jami'ar Abuja, Sebastine T. Hon. SAN, Dokta Shamsuddeen Bello, Muhammad Yusuf Abubakar (Registrar) UMYU.
Daga karshe, manyan bakin da suka halarci taron sun zagaya ginin tsangayar ta koyon aikin Lauyan dake cikin jami'ar domin ganin yadda wurin yake da irin kayan aiki da aka zuba ciki.