Irin Shugaban da ake nema A Hukumar Alhazai NAHCON

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes22042025_204016_FB_IMG_1745353680453.jpg

Daga Bilkisu Yusuf Ali

Prof Abdullahi Sale Usman tabbas shi ne irin shugaban da hukumar ta jima tana nema wurin tsantseni da kula da hakkin al'umma da tsayawa tsayin daka kan duk abin da ya zama wajibi ba tare da gazawa ko kosawa ba. Hatta a bangaren tafiyar da abokanan aiki Farfesa Abdullahi Pakistan sai dai a yi kuka da shi kan yaki bayar da kai a yi abin da bai dace ba, amma ba wai ya ki sauke nauyin ma'aikata ba. Wannan shi ne shugabanci tare da misalin abin da malam ya dau lokaci yana koyarwa a kai na kare hakkin amana. A daliilin kwazon Shugaban na NAHCON alhazan kasar nan sun sami gagarumin ragi a kujerar aikin hajji sannan ga kyakkyawan masaukai da abinci da masaukai a Makka da Madina da kuma Minna. 
Hatta a jiragan da za su yi jigilar alhazai Farfesa Pakistan bai bar alhazai a hannun rubabbun jirage ba, sai da ya tabbatar da ya zaba ya darje ya nemo jirage masu inganci da lafiya da cika alkawari. Hakika Hukumar NAHCON Ta yi abin da ya dace. Sai fatan Allah ya sa a yi lafiya a gama lafiya , Alhazanmu su yi hajji karbabbiya amin.

Follow Us