Sarkin Fulanin Joben Katsina: WANE NE SHI? SU WAYE JOBAWA?
- Katsina City News
- 24 Nov, 2023
- 780
Mu’azu Hassan
@ Katsina Times
Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman (CFR) ya amince da ba da sarautar Sarkin Fulanin Joben Katsina ga Alhaji Farouk Lawal Jobe mataimakin Gwamnan Jihar Katsina.
Wannan amincewar tana kunshe ne a cikin wata wasika da Sarkin Katsina ya sanya wa hannu a ranar 21 ga Nawumba, wadda aka shaida wa Alhaji Farouk Lawal Jobe amincewa a ba shi sarautar Sarkin Fulanin Joben Katsina.
WAYE FAROUK LAWAL JOBE?
An haifi Alhaji Farouk Jobe a shekarar 1965 a garin Kankara da ke Jihar Katsina. Ya yi karatunsa a Kankara Primary School, da Teachers College Dutsinma. Ya yi NCE a College of Education Kafanchan. Ya yi digrinsa na farko a BUK Kano. Ya yi digiri na biyu a Jami’ar Maiduguri. Ya sake yin wani digirin na biyu a kan harkar kasuwanci a Jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sakkwato.
Duk rayuwarsa ta aiki ya yi ta ne a cikin harkar Banki. Ya yi aiki a Bankuna daban-daban daga ciki har da AFRIBANK, STANDARD TRUST, UBA, da SKY BANK.
Ya yi kwasakwasai a ciki da wajen kasar nan a kan harkar Banki da tatttalin arziki. Ya shiga siyasa, inda kai tsaye ya shiga jam’iyyar adawa a wancan lokacin ta APC. Da aka kafa gwamnati, sai Malam Aminu Bello Masari ya nada shi mai ba Gwamnan Katsina shawara a harkokin Banki. A zango na biyu kuma aka nada shi Kwamishinan Kasafin Kudi da Tsare-tsare.
Jobe dan kasuwa ne, kuma manomi, yana kuma da jari a harkoki daban-daban, kuma mai kishin bunkasar ilmi. Shi ne wanda ya mallaki makarantar Ijaba da ke garin Dandagoro. Ya fito daga gidan sarautar Fulanin Jobawa da ke Kankara.
SU WAYE FULANIN JOBAWA?
Mujallar nan mai tattara tarihi da kawo su ta KATSINA CITY NEWS a fitowar ta ta watan Disamba 2021, ta yi bincike mai zurfi a kan asalin Fulanin Jobe, kuma ta yi babban labari da shi a bangonta.
Tarihi ya nuna kabilar Fulanin Jobawa sun fito ne daga wani yanki da ke kasar Morocco. Su Fulani ne masu tafiya da kiwo, noma da kuma neman ilmin addinin Musulunci.
Tarihi ya nuna sune kabilar Fulanin farko da suka fara cakudedeniya da Hausawa har ma da auratayya.
Jobawa sune Fulanin da in suka iske wuri sukan bar ’yan’uwansu su kafa mazaunin din-din-din, musamman in a wurin akwai kasar noma, ko wurin kiwo, ko wajen neman ilmin addini.
Fulanin Jobawa sun warwatsu a fadin Nijeriya, musamman a Kano, wadanda suke cikin masu nada sarautar Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe, Adamawa da Borno. Sai wani yankin Nijar da kasar Kamaru.
Fitattace a cikin Fulanin Jobawa shi ne Malam Muhammadu Bakatsine, wanda shi ne ya amso tutar jihadi a Kano a wajen Shaikh Usman Dan Fodio. Bayan an ci Kano da yaki, shi aka mika wa ragamar mulkin Kano.
Sai Malam Arzi, wanda aka fi sani da Malam Adamu Dogo, asalinsa mutumin wani gari ne mai suna Makera da ke Karamar Hukumar Dutsi a Jihar Katsina. Zuriyarsa har yanzu tana cikin garin.
Malam Arzi ya rika yawo rugar Fulani yana ilmantar da su. Ya rasu a wani gari mai suna Dan Kwari a Jihar Tawa da ke kasar Nijar.
Malam Arzai ya iske wasu mutanen Dan Kwari suna bautar aljanu, ya musuluntar da su, ya kafa makaranta da masallaci, ya zauna garin har rasuwarsa. Har yanzu yana da zuriyya a garin.
FULANIN JOBAWAN KANKARA
Tarihi ya tabbatar da cewa Fulanin Jobawa sun je garin Kankara ne a tsakanin shekarar 1690-1701 (sama da shekaru 300 da suka wuce). Sarkin Fulani na farko shi ne Sarkin Fulani Jobe, Umaru, wanda ya rike sarautar daga 1702 -1735. An yi sarakunan Fulanin har zuwa mahaifin Farouk Lawal Jobe. Sarkin Fulani Jobe Muhammad Lawal Abubakar, wanda ya rike sarautar daga 1980-2007, wanda ke rike da sarautar Sarkin Fulanin Jobe na Kankara shi ne Muhammad Aminu Lawal da yake wa ne ga Farouk Lawal Jobe.
Yanzu kuma Allah ya bai wa Alhaji Farouk Lawal Jobe sarautar Sarkin Fulanin Joben Katsina.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762