Kungiyar Tarayyar Afirka Ta Dakatar Da Nijar Daga Cikinta
- Katsina City News
- 25 Aug, 2023
- 670
Kungiyar ta ce dakatarwar za ta ci gaba har sai an dawo da mulkin farar hula
Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta sanar da dakatar da Jamhuriyar Nijar daga dukkan harkokinta saboda juyin mulkin da aka yi, har sai ta koma mulkin farar hula.
Kungiyar, a cikin wata takardar bayan taro ranar Talata, ta ce dakatarwar ta biyo bayan kin amincewar da sojoji suka yi su mayar da hambararren Shugaban Kasar, Mohammed Bazoum, kan kujerarsa.
AU ta ce, “Mun yanke hukunci la’akari da dokokinmu, da kuma yunkurinmu na wanzar da zaman lafiya da Dimokuradiyya, muna kira da a dakatar da Jamhuriyar Nijar daga dukkan harkokinta, har sai ta dawo da mulkin fara hula.
“Saboda haka, kuma kira ga dukkan mambobin kasashe da ma sauran kungiyoyin kasa da kasa da su yi watsi da wannan gwamnatin sannan su daina kowacce irin hulda da ita, saboda haramtacciya ce.”
Kungiyar ta kuma jinjina wa takwararta ta Yammacin Afirka ta ECOWAS, bisa rawar da ta ce tana takawa wajen dawo da Dimokuraɗiyya a Nijar din.