Ministan Cikin Gida Ya Jagoranci Ƴanta Bursunoni Sama Da Dubu Huɗu A Gidan Gyaran Hali Dake Kuje...
- Katsina City News
- 20 Nov, 2023
- 649
A ƙoƙarin shi na ganin an rage cinkoso a gidajen gyaran hali a Najeriya ministan cikin gida Hon. Olubunmi Tunji Ojo ya jagoranci wani shiri na musamman da yake biyan tara ga waɗanda aka yankema hukunci amma basu da kuɗin biyan tara.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da shirin Mista Ojo yace a ƙoƙarin gwamnatin tarayya na ganin an rage cinkoso a gidajen gyaran hali a faɗin Najeriya ya ƙirƙiri wani shiri na musamman Inda ya nemi kampanoni da ƴan uwa da aminan arziki da su bada tallafin kuɗi a wani asusun da aka ware a babban bankin Najeriya domin biyan tarar Mutanen da ake tsare dasu, a matsayin wani yunƙuri bada Gudummuwar su ga Al'umma.
Ministan cikin gidan, Dr Hon. Olubunmi Tunji-Ojo yace wannan shirin zai fitar da aƙalla Bursunoni 4,068 da suke gidan gyaran hali an yanke masu hukunci amma basu da halin biyan tara a faɗin ƙasar nan.
Da yake ƙaddamarwar a gidan gyaran hali dake Kuje, babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, Ministan yace duk wani da aka yanke ma tara wadda bata Gaza Naira Milyan guda ba za'a biya mashi Kuma a bashi jari domin ya koma ya riƙe kanshi da sana'ar da ya koya yayin da yake gidan gyaran halin.
Tunji-Ojo ya ƙara da cewa aƙalla akwai gidajen gyaran hali Ɗari Biyu da Hamsin da Ukku a faɗin Najeriya waɗanda aƙalla ya kamata ace Mutanen dake cikin su bai wuce Mutum 50,000” ba amma yanzu mafi ƙarancin Mutanen dake cikin su sune 80,804 wanda hakan ba ƙaramin cinkoso bane shi yasa dole sai an ɓullo da tsari mai kyau da zai magance wannan matsalar.”
“Ojo yace kimanin Naira Milyan Ɗari Biyar da Tamanin N580m ne yanzu haka aka Tara domin cimma wannan ƙudurin domin sallamar Mutanen su koma gida cikin Al'umma.