Kungiyar Kwadago NLC da TUC sun dakatar da yajin aiki
- Katsina City News
- 15 Nov, 2023
- 656
Majalisar zartaswar kungiyar kwadago ta Najeriya da kuma kungiyar ‘yan kasuwa a daren Laraba ta dakatar da yajin aikin da suke yi.
Kungiyoyin sun ce dakatarwar ta biyo bayan tsoma bakin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu.
Wakilinmu ya tattaro cewa taron wanda ya fara ‘yan mintoci kadan da karfe 7 na dare ya dauki kusan sa’a guda inda kungiyoyi daban-daban da na jihohi suka yi bitar sakamakon taron da shugabannin kungiyar suka gudanar da Ribadu.
Mataimakin shugaban TUC na kasa, Tommy Etim ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a Abuja.
Sunce "Mun janye yajin aikin ne bisa tattauna da fahimtar juna a tsakanin mu da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.” Inji shi.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa shugabannin kwadagon sun gana da Ribadu tare da Ministan Kwadago, Simon Lalong a ofishin NSA a ranar Laraba da yamma.
Ofishin na NSA ya sanar da cewa an kama mutanen da suka daka wa Ajaero Duka
Kungiyar kwadagon tayi zanga-zangar nuna rashin amincewa da cin zarafin shugabanta na kasa, Joe Ajaero, da gazawar gwamnati wajen aiwatar da wasu yarjejeniyoyin da aka cimma a ranar 2 ga Oktoba, 2023 yadda ya kamata.