ƳAN BINDIGA SUN KAI HARI KATSALLE TA BATSARI
- Katsina City News
- 24 Aug, 2023
- 883
Misbahu Ahmad
@ Katsina Times
A daren jiya talata 21-08-2023 ƴan bindiga suka kai hari wani ƙauye mai suna Katsualle dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina. Ƙauyen yana kusa da shataletalen ziro ziro da unguwar magama cikin garin Batsari akan hanyar Jibiya, kusa da mazaunin jamian sojoji.
Sun saɗaɗo sun faɗa gidajen mutane ba tare da sunyi harbi ba, suka ɗauki mata biyar. Lokacin da aka farga an sanar ma sojoji, inda suka bisu har yammacin Gobirawa amma basu same su ba sai dai mutane sunji ƙarar rurin bindigu kamar ana fasa dutse da nakiya.