Dangantaka tsakanin Karim Benzema da kocin Al-Ittihad Nuno Espírito Santo ta yi tsami...
- Katsina City News
- 23 Aug, 2023
- 628
Kociyan yana ganin Benzema bai dace da salon wasansa ba kuma ya ce bai taba nemansa ya koma kungiyar ba!
Karim Benzema ya amince da Saad Al-Ladidh, wanda shine ke hulɗa da kwantiragi kuma shine wanda ya iya shawo kan Benzema ya koma Saudi Arabia, Al-Ladidh ya ce bai ji dadin halin Nuno Espírito ba, Saboda baya kula da kwarewar dan wasan.
Benzema ya nemi a ba shi kambum kyaftin din kungiyar amma kociyan ya ba Romarinho, don haka dan kasar Faransa bai zo atisaye a safiyar yau ba.
Nuno Espírito Santo ya soki Al-Ittihad cewa Benzema bai dace da salon wasansa ba kuma ya ce bai taba neman sa a kungiyar ba.
Hukumar kula da Al-Ittihad ta yi wa kocin dan kasar Portugal barazanar soke kwantiraginsa idan Benzema bai dawo atisaye ba. (Moyen-Orient)
© Fagen Wasanni