Na Miƙa Wa Tinubu Saƙon Sojojin Nijar —Abdulsalami
- Katsina City News
- 23 Aug, 2023
- 627
Janar Abdulsalami ya ce ya miƙa wa Tinubu buƙatun sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar
Tsohon Shugaban Mulkin Sojin Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar, wanda ya gana da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar, ya ce ya isar da sakonsu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, jagoran majalisar shugabannin ƙasashen ƙungiya ECOWAS.
Abdulsalami wanda yake cikin tawagar ECOWAS da ta samu ganin hamɓararren shugaban ƙasar Nijar Mohamed Bazoum da sojojin ke ci gaba da tsarewa ya ce ya kuma yi wa Tinubu bayani kan buƙatun sojojin da ECOWAS ke neman su koma bariki su miƙa wa Bazoum kujerarsa.
Ya bayyana kwarin gwiwa cewa za a warware dambarwar shugabancin na Nijar ta hanyar diflomasiyya ba ta ƙarfin soji ba, idan shugabannin ECOWAS suka zurfafa tunani sannan suka aiwatar da shawararin da ke kunshe a rahoton da kwamitinsa ya mika musu bayan dawowa daga Nijar.
Janar Abdulsalami ya sanar haka ne bayan taron da Tinubu ya kira na masu ruwa da tsakin ECOWAS kan dambarwar Nijar, inda wakilan na ƙungiyar suka yi musu bayani kan yadda ganawarsu ta kasance da sojojin da suka yi juyin mulki.
Ya ce duk da cewa ECOWAS na duba yiwuwar ɗaukar matakin soji idan masu juyin mulkin sun ƙi miƙa wuya, ba ya tunanin abin zai kai ga haka kafin ɓangarorin su daidaita.
Kwamitin Abdulsalami ya samu ganawa da sabuwar gwamnatin sojin Nijar ne a makon da ya wuce bayan da farko sojojin sun ƙi tattaunawa da su saboda takunkumin da ECOWAS ta sanya wa ƙasar kan juyin mulkin.
Ƙungiyar ta yi barazanar ƙwato mulkin ƙasar da ƙarfin sojoji har ta sanya wa sabuwar gwamnatin takunkumin karya tattalin arziki tare da yanke hulda, wanda sojojin suka yi watsi da shi a matsayin haramtacce tare da sanar da shirin yaƙi da duk ƙasar da ta nemi auka wa Nijar ta ƙarfi.
Bayan manyan hafsoshin ECOWAS sun yi ittifaƙin kafa rundunar ko-ta-kwana ta ƙwato mulki a Nijar ce, sojojin ƙasar suka ce a shirye suke, har suka sanar da samun tallafin jiragen yaki daga kasar Burkina Faso.
A ranar Asabar ta tura kwamitin Abdulsalami zuwa birnin Yamai, inda bayan ganawarsu da jagoran gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya sanar da shirinsu na miƙa gwamnati ga farar hula cikin shekara uku, matakin da ECOWAS ta yi watsi da shi.
Kwamishinan harkokin siyasa da zaman lafiya na kungiyar, Abdel-Fatau Musa, ya ce ƙungiyar ba ta son gwamnatin rikon kwarya a Nijar ta kai shekara daya.