Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta samu nasara kame mutane 134 da ake zargi da laifuka daban-daban a watan Oktoba
- Katsina City News
- 02 Nov, 2023
- 824
Zaharaddeen Ishaq Abubakar
A wani gagarumin baje kolin tabbatar da doka da oda, rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta samu gagarumin ci gaba wajen dakile miyagun laifuka a cikin watan Oktoba na shekarar 2023. Rundunar ta bayar da rahoton manyan laifuka guda saba’in da biyar da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane, da kuma kisan kai. An shigar da kararraki saba'in da biyu a gaban kotu, inda aka kama mutane 134 da ake tuhuma.
Nasarorin sun hada da ceto mutane ashirin da uku da aka yi garkuwa da su, da kuma kwato wasu makamai kamar bindiga kirar turawa da harsashi mai rai, da kuma wani babur da ake zargin na sata ne. Bugu da kari, an kama wasu mutane biyu da ake zargi da kashe dan sanda, barayin shanu, masu garkuwa da mutane, da kuma ‘yan fashi da makami a ranar 17 ga Oktoba, 2023, ta hanyar sahihan bayanan sirri.
A wani samame na daban a ranar 13 ga Oktoba, 2023, an kama wasu mashahuran masu garkuwa da mutane biyu. Wannan ikirari nasu ya ba da karin haske kan yadda suke da hannu wajen yin garkuwa da mutane da yawa domin neman kudin fansa, wanda ya kai ga kwato makudan kudade na kudin fansa.
A ranar 26 ga watan Satumba, an kama wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, dag bayanen da suka yi aka samu nasarar kwato dukiyoyin da aka sace, ciki har da wayoyi da kuma abin hawa.
A wata gagarumar nasara, an kama wasu mutane uku da ake zargi da yin garkuwa da mutane a ranar 14 ga watan Oktoba, 2023, lamarin da ya kara inganta harkokin tsaro a karamar hukumar Funtua da kewaye.
Yunkurin da rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ke yi yana haifar da Ɗa mai ido inda ake samun raguwar miyagun laifuka a jihar. A wata takarda da mai magana da yawun rundunar ta 'yan sanda Sadiq Abubakar ya rabawa Manema Labarai ta tattaro duka bayanai dalla-dalla akan ayukan rundunar na watan da ya gabata.