Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Taron Sanin Makamar Shugabanci A Rwanda
- Katsina City News
- 23 Aug, 2023
- 736
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal zai bar Abuja zuwa Kigali ta ƙasar Rwanda domin halartar taron sanin makamar aiki da aka shiryawa shugabanni.
Taron zai samu halartar sauran gwamnonin Nijeriya wanda shirin Majalisar Ɗinkin Duniya na UNDP ya shirya daga ranar 24 zuwa 27 na watan Agusta.
A wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idria ya fitar, ya ce taron haɗin gwiwa ne tsakanin UNDP da Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya.
Ya ƙara da cewa, a yayin taron za a yi kwasa-kwasai da kuma ziyarce-ziyarce masu fa'ida.
Ya ce: "Wannan taron an shirya shi ne don ƙara wa shugabanni sani kan makamar aiki, wanda kuma zai ba su damar zagaya birnin Kigali domin su ga yadda tsarin bunƙasa biranai ya ke.
"Wannan zagaye don ganin yadda aka gina Kigali zai ba gwamnoni dama, musamman ma dai Gwamna Lawal wanda a 'yan kwanakin nan ya ƙaddamar da aikin sabunta biranai a birnin Gusau.
"Haka nan kuma taron zai ba shugabannin dama wurin tattauna muhimman batutuwa da za su amfani jihohinsu.
"Taron zai buɗe hanyoyin da za su amfani al'umma, musamman kan zuba hannun jari da kuɗaɗen shiga."