AGILE da Hukumar Ilmi ta jihar Katsina sun shiryawa Dalibai Taron Karfafa gwiwa a shiyoyi 3 na jihar Katsina

top-news

Ma'aikatar Ilmi ta jihar Katsina hadin gwiwa da Gidauniyar samar da Ilimin 'Ya'ya Mata (AGILE) ta shirya wa daliban jihar Katsina Bita, a Bikin ranar Ilimin Mata ta Duniya 

Zaharaddeen Ishaq Abubakar

Taron wanda ya hado 'yan Makarantar Sakandare daga kananan hukumomin shiyyar Funtua 11, an zabo hazikan Dalibai kimanin 150 domin Tattaunawa da kuma Jin ta bakinsu akan Matsalolin da ke hana yara zuwa Makarantar da kuma bada shawara da jan hankali akan Ilimin 'Ya'ya Mata.

Dokta Mustapha Shehu Ph.D Shine Shugaban Shirin na (Adolescent Girls Initiative Learning and Empowerment) AGILE Project a jihar Katsina, wanda a bisa jagorancinsa taron ke gudana, Katsina Times sun tattauna da shi, kuma yayi karin haske akan manufar wannan shiri, inda ya bayyana cewa. "Akan yi amfani da ranar 11 ga watan Oktoba na ko wace shekara domin tunawa da ranar Ilimin 'Ya'ya Mata, da kuma kira ga Gwamnati da masu ruwa da tsaki, da sauran al'umma don tallafawa da tabbatar da an cigaba da bada goyon baya don 'Ya'ya Mata su samu Ilimi mai inganci kamar yanda kundin tsarin mulkin kasa ya tanadar, Irin yanda suma 'ya'ya Maza suke dashi".

Dokta Shehu ya ce, " A yau 25 ga watan 10 mun tara yara Maza da mata su 150 daga kananan hukumomi 11 da suke a yankin Funtua don huras da su, amfanin bin dokokin kasa, a makaranta da kuma sanin hakkokinsu da 'yancin su akan Ilimi, da kuma yanda zasu gano yaran da basu zuwa makaranta da koya masu dubarun da zasu yi don su jawo hankalinsu akan su dunga zuwa makaranta".

Dokta Mustapha Shehu ya kara da cewa, shirin zai dunga agazawa yaran da rashi ko hali na rayuwa yasa suka gaza zuwa makaranta don tallafamasu da scholarship don cigaba da karatunsu. Yace "wannan na daya daga cikin shirye-shiryen da AGILE ke yi tun shekarar farko da aka farashi zuwa yanzu, domin a tabbatar da cewa yara maza da mata an basu hakkinsu na cigaba da zuwa makaranta, ta hanyar gyaran makarantu da gina sabbi da horas da malamai da kuma samar da kayan koyo da koyarwa da duk wani tallafi da makarantun ke bukata da zai samar da yanayi mai kyau da zai sa dalibai su zauna suyi karatu a makarantu su kuma malamai su samu jin dadi gamsasshe wajen koyar da darussan su.

Tun da farko Dokta Mustapha Shehu ya yi jawabi ga daliban akan abinda duka taron na wuni daya ya kumsa da kuma yanda aka farashi tun daga yankin Katsina har zuwa a yanzu wato Funtua Zone.

Hajiya Hadiza Usman tayi jawabi na kwantar da hankali ga daliban da kuma jawo hankalinsu akan su natsu su ji kuma su bada shawara bisa ga abinda suka ji, tace ta hanyar shawarwarinsu ne, za a iya gano wata matsalar da za a kauda ita domin cigaban ilimin.

Hajiya Binta Abdulmumini ita ta gabatar da jawabi mai tsawo akan GBV wato Gender Based Violence gami da tambayoyi da amsoshi.

Da yawa daga cikin dalilan sun bayyana dalilan da suke gani yana hana zuwa makaranta ga yara, kuma dalilin sun rabasu bangarori uku.

Bangare na farko sune Iyaye: wasu Iyayen basu da karatu, don haka ba kasafai suke jin zafin rashin karatun 'ya'yansu ba. Shiyasa suke ko in kula ga karatun na 'ya'yansu. Suka ce, sunfi maida hankali ga kasa masu Talla ko aikin gona, ko kuma su bar yaran su nemi mafita da kansu.

Na biyu a bangaren Malamai, yaran sun bayyana irin yanda Malaman makarantu suke hukunci mai tsanani ga yaran da sukai laifi ta dalilin haka yara suke gudun Makaranta har ma na waje wadanda basa yin makarantar suji basa sha'awar karatu, ko kuma malamai masu cin zarafin musamman Mata, suna nemansu ta hanyar da bata dace ba.

Sai na uku kuma su kansu yaran duk wanda ya gamu da abokan banza to basu tunanin komai sai abinda abokan nasu suka dorasu akai.

Wasu daliban sun kawo dalilin cewa, wasu yara basu da iyaye duk sun mutu, don haka ne ba zasu samu gatancin da za a tallafa masu ba don su samu damar yin karatu.

Sannan kuma  bayan Damuna idan an cire amfanin gona, yara na zuwa tsintar ragowar abinda yayi saura bayan kwashe amfanin gona ana kiran wannan da suna (Kala) suka ce wannan na hana yara zuwa makaranta a wannan yanayin.

Matsalolin da daliban suka bayyana ya jawo hankalin kusan dukkanin malaman da suka halarci taron inda kowa ya dunga mamaki gami da rubutawa domin tattaunawa matsalar don samun mafita.

An gudanar da taron ne a babban takin taro na Assembly Hall dake makarantar Gwamnati wato Government College Funtua

NNPC Advert