ƁARAYIN DAJI SUNKAI MUNANAN HARE-HARE A YANKIN BATSARI
- Katsina City News
- 25 Oct, 2023
- 909
Misbahu Ahmad Batsari
@ Katsina Times
A daren ranar talata 24-10-2023, ɓarayin daji ɗauke da muggan makamai suka kai hari wani ƙauye mai suna Tsagengeni dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Ɓarayin dake kan babura sunyi ma garin ƙawanya tare da harbin kan mai uwa da wabi, wanda nan take suka kashe mutane ukku, amma daga baya mutane biyu sun ƙara rasuwa yayin da aka garzaya da su asibiti, kuma har yanzu akwai ƙarin mutane huɗu dake kwance a asibiti ana yi masu magani.
Sannan ɓarayin sun kora garken shanu da suka samu a wani gida wanda wani mazaunin garin ya bayyana mana cewa shanun na ajiya ne aka kawo daga wani ƙauye.
Haka kuma ƴan fashin daji sunkai hari ƙauyen Garin Waziri dake cikin yankin na Batsari a ranar asabar 22-10-2923 da dare inda suka kashe wani bawan Allah mai suna Alhaji Sale Garin Waziri wanda suka baƙaci ya basu kuɗin da ya saida ammafin gonarsa, amma basu samu ba suka harbe shi, sannan suka kwashi matan garin guda biyar suka yi garkuwa da su.
Katsina Times
Www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779