Shugaban Kungiyar Izalatul Bid'a Wa'ikamatu Sunnah ta Kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau yayi kira ga Musulmin Nijeriya da su sanya Al'ummar Palestinu Addu'a

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 23,10,2023

Sheikh Abdullahi Bala Lau Shugaban Kungiyar Izalatul Bid'a Wa'ikamatu Sunnah mai Headquarter Kaduna ya bayyana kiran nasa ne a lokacin gudanar da wa'azin kasa a Katsina ranar Lahadi.

Shihin Malamin yayi Allah wadai kan kisan da yace yahudawa na aikatawa akan Palestinu idan ya bayyana yahudawa a matsayin Azzalumai da fasu san hakkin Dan'adam ba, yace "yana kira ga Ahlus-sunah na fadin Najeriya da ma dukkanin Musulmi da su dukufa addu'o,i na Neman Nasara ga Palestinu masu rauni domin samun galaba akan makasansu da masu goya masu baya.

Shugaban Izalar na Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau ya kuma bayyana Matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya a matsayin wani kalu-bale babba da yace dole sai an tashi tsaye, yace ba gwamnati ba kadai, dukkanin al'umma su fito su taimakawa Gwamnati da jami'an tsaro don kawo karshen matsalar.

Lau ya kuma tabbatar ma Al'umma cewa zasu shiga Daji inda wadannan 'yan uwa nasu Filani suke zaune  yi masu wa'azi ko Allah ya sanya su shiriya.

Yace "dukkanin wani dan Ahlus-sunah baiga zama ba dole ne mu yi masu wa'azi kuma zamu shiga Daji, mu fadi masu Allah ya ce, Annabi (S) yace idan zasu shiriya su shiriya idan ba zasu shiriya ba, a kashe su, don haka Allah yace.

A karshe ya yabawa Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda akan irin kokarin da yake na ganin tsaro ya wadata a jihar Katsina.

Taron wa'azin na kasa da ya gudana a kwanaki uku daga 19 ga watan Oktoba zuwa 22 ga watan Oktoba an masa taken "Yaki da Talauci, Yunwa da Ta'addanci" Malaman Addinin Musulunci fiye da 30 ne suka gudanar da wa'azozin akan haka daga fadin Najeriya bayan Khuɗba a Masallatan Juma'a daban-daban na garin Katsina, sana aka rufe gagarumin wa'azin a filin wasa na Abdulmumini Aminu Stadium dake cikin Birnin Katsina.

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda shine babban bako a wajen da sarakunan Katsina da Daura inda suka Turo da wakilansu da sauran Kwamishinonin Gwamnatin jihar Katsina.

NNPC Advert