Kungiyar kare Hakkin dan Adam mai suna IHRAAC ta zargi hukumar Kula da ababen hawa KASROTA a Katsina da cin hanci da rashawa gami da take hakki
- Katsina City News
- 19 Oct, 2023
- 1185
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 19/10/2023
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa (IHRAAC) ta nuna damuwa kan hukumar kiyaye haddura da zirga-zirga ta jihar Katsina KASROTA. Kungiyar IHRAAC mai fafutukar tabbatar da zaman lafiya da kare hakkin dan Adam ta bayyana batutuwa da dama dangane da KASROTA.
Kungiyar ta (International Human right Awareness and Advocy Center IHRAAC) a turance ta bakin Shugaban Kungiyar na Ƙasa Dr. Salisu Musa a wata takarda da ya rabawa Manema Labarai ya kawo zarge-zage da dama da suke yiwa hukumar akan cin hanci da rashawa, saba Doka da tsananta Tara, da ta wuce kima, akan masu ababen hawa.
Sanya Tsoro ko razani a yayin mu'amala a tsakanin jami'an KASROTA da Al'umma, wanda hakan na haifar da kin bin Dokokin hanya.
Haka zalika Dakta Salisu Musa ya Zargi hukumar da sanya Tara mai tsanani akan duk wanda yazo hannu, kuma hakan yana haifar da rashin jituwa.
Kungiyar ta IHRAAC ta yi kira ga Gwamnatin jihar Katsina da Majalisar Dokokin jihar da su duba Lamarin hukumar KASROTA domin ganowa da kuma hukuntawa gami da kawo gyara a cikin duk wani rashin Ɗa'a da Cin hanci ko cin Zarafi a cikin hukumar ta KASROTA
Aiwatar da gaskiya, Kyautata Mu'amala a tsakanin al'umma da kaucewa sanya Tara maras kangado. Kungiyar ta yi kira ga Gwamnati da ta samar da wani sashi na hadin gwiwa da zai bawa jami'an Ingantacciyar Horaswa, da fadakar da al'umma akan Dokokin hanya da zirga-zirga don samun fahimtar juna a tsakanin KASROTA da su.
IHRAAC ta yi imanin cewa magance wadannan matsalolin da kuma aiwatar da wadannan shawarwari za su taimaka wa hukumar ta KASROTA ta cimma burinta na samar da hanyoyin tsaro, da mutunta dokokin zirga-zirga a jihar Katsina.