Gwamnatin jihar Katsina zata hada hannu da hukumar NDLEA don yaki da masu ta'ammuli da miyagun kwayoyi
- Katsina City News
- 18 Oct, 2023
- 896
GWAMNATIN JIHAR KATSINA ZA TA HADA HANNU DA NDLEA DON YAKI DA MASU TU'AMMALLI DA MIYAGUN KWAYOYI
Gwamanatin jihar Katsina ta sha alwashin ci gaba da hada karfi da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wato NDLEA wajen magance matsalar tu'ammali da miyagun kwayoyi a cikin jihar.
Sakataren gwamnati jihar, Barrister Abdullahi Garba Faskari ya bada tabbacin hakan a yayin da ya karbi Mataimaki na musamman ga shugaban hukumar na kasa, Kanar Yakubu Bako mairitaya, a ofishinsa a madadin Gwamna Dikko Umaru Radda.
Barrister Abdullahi Faskari ya ce gwamnatin jiha da NDLEA suna aiki tare domin ganin an magance masu fataucin kwaya da mashayanta a cikin alumma.
Ya kuma amsa gayyatar da hukumar ta yi ma Gwamna Dikko Radda na ya kasance babban bako na musamman a wajen bukin yaye dakarun NDLEA da suka kammala samun horo akan dabarun kawo karshen matsalar shaye - shaye da ta addabi matasa.
Tun farko Mataimaki na musamman ga shugaban hukumar NDLEA, Kanar Yakubu Bako mairitaya ya bayyana irin tsare - tsaren da suka yi na shirin yaye sabin jami'an da suka samu horo.
Kanar Bako wanda tsohon gwamnan soja ne na jihar Akwa Ibon, ya ce ya zo ne da kan sa domin ya gayyaci gwamnan, zuwa bukin yaye jami'an hukumar wanda za a yi ranar Alhamis din nan, 19/10/2023 a Makarantar Sibil Difens, (NCSDC) dake kan titin Batsari, a nan Katsina.
Kanar Yakubu Bako ya kuma yi godiya ga gwamnatin jihar Katsina a karkashin jagorancin Dr Dikko Umaru Radda bisa ga irin tallafin da take baiwa hukumar NDLEA dake nan Katsina.
Ya yi kiran da aka hada karfi da karfe domin magance illolin da masu saida kwaya ke haddasawa a cikin al'umma.
Daga karshe ya jinjina ma Gwamna Dikko Ummar Radda akan namijin kokarin da ya yi na kafa dakarun da za su taimaka wajen ganin an kawo karshen matsalar tsaro a fadin jahar nan, wato CWC.