Gwamnatin jihar Katsina ta biya Malaman tsangaya Alawus din Watanni biyar, fiye da Naira Miliyan Talatin da Takwas

top-news

Gwamnatin jihar Katsina ta ware Naira Miliyan 38.9 domin biyan Malaman tsangaya Alawus din wata biyar.

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 

Gwamnatin Malam Dikko Umar Radda ta ware kudin ne Naira Miliyan Talatin da takwas da dari tara don biyan Alawus din Malaman Makarantar Allo wato tsangaya, biyan Alawus din da yake gudana yanzu haka a karkashin Hukumar Ilimin Manya wato Agency for Mass Education Katsina.

Kwamitin kula da bayar da Alawus din bisa Jagorancin Babban Daraktan Ma'aikatar Alhaji Aliyu Lawal Tambura da Hajiya Bilkisu Ado Shinkafa Coordinator Egency for Mass Education, a yankin Katsina wato (Katsina Zone).

Hajiya Bilkisu Ado Shinkafi ta bayyana jin dadin ta dongane da yanda tsarin bayar da Alawus din yake gudana, inda ta ce sun fara da Daura Zone, Funtua Zone, yanzu kuma gasu a Katsina Zone, tace Aikin yana guda Lafiya lau kuma cikin tsari.

Da yake jawabi ga manema labarai, Babban Daraktan Hukumar Ilimin Manya na jihar Katsina Alhaji Aliyu Lawal Tambura ya bayyana cewa "wannan kudi da suke biya na wata biyar ne da aka yi ba a biya ba, sakamakon canjin gwamnati da aka samu, amma yau cikin ikon Allah an hada kudin su na wata biyar da aka yi ba a biya ba, an biyasu a yau.  

Tambura ya yaba da irin kokarin gwamnatin jihar Katsina da Kwamishinan Ilimi, tare da Mai taimaka wa Gwamnan Katsina akan Ilimi, wanda ya jajirce da kuma sanya ido akan komai ya tafi daidai a dukkanin kananan hukumomin jahar Katsina.

Yace "da yardar Allah, da a cigaba da biyan Malaman Alawus dinsu  na wata-wata kamar yanda aka saba, kuma mutanen da muke biya a duk wata sune mutum dubu daya da dari shida da sittin da hudu, (1664) dama abinda ya jawo wannan tsaikon Sabuwa gwamnati ce da ta shigo" inji shi.

A Zantawar mu da Malaman Makarantun na Allo (tsangaya) sun bayyana jin dadin su, bisa wannan kudade da aka basu, kuma sunyi kira ga Gwamnatin Malam Dikko Umar Radda da ya duba yiyuwar kara masu bisa abinda ake basu a yanzu, suka ce duba da yanayin rayuwa da ake ciki.

Malam Dahiru Lawal Jifatu, daya daga cikin Malaman tsangaya da ya amshi Alawus dinsa na wata biyar ya bayyana jin dadinsa, sana kuma yace suna iya kokari na ganin sun samar da tsarin koyarwa da inganta shi, yace bisa jajircewar su, yasa yanzu haka a cikin daliban da suke koyamwa an fara yaye masu PhD, kuma a dalilin shigar da tsarin Zamani a cikin koyarwa, yace suna godiya kwarai da gaske.

An gudanar da shirin bayar da Alawus din ne a ranar Laraba 18 ga Watan Oktoba, a cikin tsohuwar ma'aikatar Ilimi ta E.A dake kofar Sauri a cikin garin Katsina.