Sabbin Kwamishinoni da Masu Madafun Iko, Babbar Matsalar Itace...
- Katsina City News
- 21 Aug, 2023
- 828
Zaharaddeen Ishaq Abubakar
Maganar tawa tana Nufin Ko'ina a Jihohin Arewaci dama Ƙasar Najeriya gaba ɗaya, Amma zan karkata Tambihin a jihar da nafi sani, wato Katsina. Saidai rubutun yana nufin Duka jihohin Najeriya.
A ƙasa da watanni biyu da suka gabata mafiya yawa daga jihohin Najeriya sun gudanar da Naɗe-naɗe (wasu ma suna kan gudanarwa) tun daga Kwamishinoni zuwa Mataimaka na Musamman da zasu dafama Gwamnoni domin raya ƙasa da kawo cigaban jihohinsu.
Abin nufi a wannan muƙaman da Gwamnonin ke naɗawa shine, su gudanar ko su gabatar ko su aikata ko su yi wani abu na ci-gaba a madadinsu, a hukumar da suke kula da sanya ido akai. Anan wata Hukumar Samowa za'ayi, wata kuma Samarwa za'ayi wata kuma duka za'a samar za'a samo. Wato Kamar Misalin Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji Mafi yawa tana Samowa ne, ba Samarwa ba, Idan anbi ta wata hanyar da bata da bukatar dogon jawabi sai muce duka.
Sabanin hukumar Ilimi ko ta Lafiya da suke samar da Ilimi da ingantacciyar Lafiya a cikin Al'umma. Wato abinda suke samarwa yafi abinda suke samowa idan aka kwatanta ta da hukumar Tattara Haraji.
Mafiya yawa Ofisoshin mataimaka na Musamman su kuma, suna Amsa ne ma daga wajen Gwamnati, Ila iyaka kawai ace suna Tuntuɓa Gwamna bisa bagiren da ya dace domin gudanar da Mulkin Al'umma.
Gwamnati na iya ƙoƙari wajen zaƙulo Mutane masu Ƙwazo Zuciyar Aiki da Hazaƙar Aikin, Misalin Gwamnatin da nake kusa da ita, ta Malam Dikko Umar Radda na Katsina. A bincike da kuma irin tattaunawa da nayi da wasunsu, baki da baki, lallai suna da kyakkyawar Aniyar kawo gyara da cigaba a ofishin da aka damƙa masu wakilcin amanar al'umma, sai 'yan ƙalilan da ba'a rasa ba. (Wanda kuma a fahimta ta ambasu ladan Aikin kafa Gwamnati ne ba don sun Cancanta ba wannan kuma ko a wace Gwamnati ana samun haka.)
Saman tayi kama da Ƙasan sai an shiga ake ganewa
A lokacin yaƙin neman zaɓe 'Yan Siyasa suna ɗaukar kaya masu nauyi kuma suyi alkawarin ɗorawa aka, ba tare da sun Jinjina nauyin ba. Shi yasa ma zakuga an taso rigi-rigi sakat, a ƙarshe har talaka ya fara maida magana.
Sauran Masu muƙamin naɗi da suke taimakawa Gwamnatin suma suna shiga cikin irin wannan yanayin na ɗauka da ajewa, amma su mafiya yawa rashin isassun kuɗin gudanarwa sune ke hanasu komai.
Komin kishinka komai kake so a cigaba a ma'aikatarka idan har Gwamnatin da ta ɗoraka bata iya fita hakkin ma'aikatar yanda ya kamata ba, dole ma'aikatar ta mutu ko tayi bacci ko wani abin da ake hanƙoro ya tsaya babu yanda ka'iya.
Da yawa daga cikin Kwamishnoni ko Manyan Daraktoci da ake turawa ma'aikatu idan suka isa ma'aikatar suna iske tarin matsaloli wanda kishinsu yasa suce sai sunga bayan matsalar, akarshe rashin bada isassun kudin gudanarwa daga gwamnatin yasa ita matsalar taga bayansu.
Banaso in tsawaita saboda mutane nada raunin karanta rubutu, amma zan kulle zancen nawa dacewa, Kwamishinoni, Daraktoci, Sakatarori, da sauran masu madafun iko, ku duba abinda ke yiyuwa kuyi, don kawo gyara da ci-gaba. Ba komai bane Gwamnati ko Gwamna zai iya aiwatarwa shima saboda saɓanin abinda ya zata, ko da yake Farkon Mulki akwai Zaƙi, amma a ƙarshe dai kam ɗaci yake komawa. Don haka shima gani yake kamar komai zai iya, sai dai musani "Tula Bata Shuri" sai kulasa miyarku Lami-lami. Dafatan Allah ya maku jagora ya shige maku a gaba ya bada ikon sauke nauyi idan an ɗauka.