Karfafa Tsaro: Gwamna Radda Ya Kaddamar Da 'Katsina Community Watch Corps
- Katsina City News
- 10 Oct, 2023
- 1143
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 10/10/2023
A wani gagarumin yunkuri na magance matsalar tsaro da ke kara kamari a jihar Katsina, Gwamna Malam Dikko Umar Radda ya gabatar da wata rundunar tsaro ta musamman da aka fi sani da ‘Katsina Community Watch Corps’ a wani gagarumin biki a ranar Talata.
Gwamna Radda, a lokacin da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da jami'an, ya jaddada kudirin sa na cika alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabe na inganta harkokin tsaro a fadin jihar.
Don tabbatar da tsaron jihar Katsina Gwamna Radda ya bayyana cewa, “Ko da hakan na nufin za'a kashe kasafin kudin jihar gaba daya kan harkokin tsaro, za mu maido da zaman lafiya da tsaro. Kaddamar da wannan shiri yace shine na farko.
Gwamnan ya roki matasan jami’an tsaron da su gudanar da ayyukansu cikin kwazo da kwarewa, inda ya jaddada bukatar sake farfado da martabar jihar.
Taron kaddamar war ya kunshi jami’ai 1500, da kayan aikin yaki da ta’addanci, Gwamna Radda ya samar da motocin yaki masu sulke, motocin Hilux 70, da babura 700.
An gudanar da gagarumin bikin kaddamar war ne a babban filin wasa na Muhammadu Dikko da ke birnin katsina wanda ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen jihar. Manyan bakin sun hada da gwamnonin Kaduna, Kano, Zamfara, Jigawa, Kebbi, da Sokoto.
Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Alhaji Ahmed Rufa'i, daraktan hukumar leken asiri ta NIA, mataimakin sufeto janar na 'yan sanda, da wasu manyan mutane ne suka halarci bikin.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sarkin Katsina Dr. Abdulmumini Kabir Usman CFR da Sarkin Daura Dr. Umar Faruq Umar CON, ‘yan majalisun jiha da na tarayya, da jami’an gwamnati daban-daban.