Al'umar Badawa sunyi Bikin cika shekaru dari Biyu da doriya da shigowar su Kasar Katsina
- Katsina City News
- 07 Oct, 2023
- 991
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Asabar 7 ga watan Oktoba 2023 ne Al'umar Badawa 'Yan Asalin jihar Yobe, da suka shigo Katsina tun a karni na 18 kimanin shekaru dari biyu da ashirin da wani abu.
Alhaji Abba Yusuf Funtua shine shugaban al'umar Badawa Yan jihar Katsina, kuma shugaban taro, a madadin Al'umar ta Badawa ya gabatar da jawabin maraba da bakin da suka shigo jihar Katsina da Badawa na jihar Katsina.
Manyan Baki da suka halarci taron akwai, Sardaunan Bade, tsohon shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Dakta Ahamad Lawan, da tawagar sa, tsohon Ministan Jiragen Sama na Nijeriya Alh. Hadi Sirika, Al'ummar Badawa daga Jihar Yobe, Hakimman Masarautar Katsina, da na Yobe, Muƙarraban Gwamnatin jihar Yobe da sauran su.
Mnyan Malamai Furofesoshi da jami'o,in Najeriya suka gudanar da Kasidu a wajen taron, inda wasunsu suka bayyana Asalin Al'ummar Badawa, Tarihin su, da kuma Kafuwar Sarautar su, a jihar Yobe, wasu suka gudanar da Kasidar zuwan Badawa a Birnin Katsina , sarautun da suka rike da kuma gwagwarmayar da sukai don kawo cigaba a jihar dama kasa baki daya.
Taron ya gudana a Babban Dakin Taro ma'aikatar Kananan Hukumomi.(Local government Service Commission) dake kan titin zuwa Kaita a Birnin Katsina.