Ƙungiyar ƙwadagon Ghana na adawa da tura sojoji Nijar
- Katsina City News
- 21 Aug, 2023
- 1132
Kungiyar Kwadago mafi girma a Ghana ta yi gargadi kan yin amfani da karfin soji wajen kawo karshen juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar.
Kungiyar ta tabbatar da cewa, hanyoyin diflomasiyya za su iya dawo da tsarin mulki a Nijar matukar shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (Ecowas) suka tattauna da gwamnatin soja ta hanyar da ta dace.
Sakatare-janar na ƙungiyar ƙwadagon, Yaw Baah ya bayyana cewa, "Mun yi imani da gaske cewa duk wani yunkuri na tilasta wa gwamnatin mulkin soji da Tchiani ke jagoranta a Nijar zai kara dagula al'amura da rashin tsaro a yankin."
Kungiyar Ecowas da ke yammacin Afirka ta bayyana yiwuwar daukar matakin soji kan gwamnatin mulkin soja da ta hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.
Yayin da gwamnatin mulkin sojan kasar ta bayyana aniyarta ta nayar da mulki ga farar hula cikin shekara, lamarin da kungiyar ta Ecowas ta ƙi amincewa da wannan shawara.
Dangane da juyin mulkin, Ecowas ta kakaba wa Nijar takunkumi, wanda ya yi tasiri ga tattalin arzikin kasashe makwabta, kamar Ghana.
‘Yan kasuwar Ghana sun bayyana kalubalen da suke fuskanta wajen shigo da kayan lambu musamman albasa daga Nijar, lamarin da ya janyo tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki.
Ghana dai ta dogara ne kacokan a kan Nijar da kusan kashi 70 cikin dari na albasarta da take shigowa da ita.
A shekarar 2021, Nijar ta fitar da albasar kusan dala miliyan 23 zuwa Ghana da sauran kasashen yammacin Afirka.