ECOWAS Ta Umarci Dakarunta Su Dauki Matakin Soji A Kan Nijar
- Super Admin
- 10 Aug, 2023
- 450
Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta umarci dakarunta da su kasance cikin shirin dawo da gwamnatin farar hula a Jamhuriyar Nijar.
Shugaban kungiyar, Omar Alieu Touray, ne ya sanar da hakan yayin da yake karanta matsayar da taron kungiyar ya cim ma a Abuja, kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar a watan da ya gabata.
Ya ce kungiyar ta kuma yi kira ga Kungiyar Hadin Kan Afirka (AU) da sauran kungiyoyi da su goya mata baya kan matakin da ta dauka.
ECOWAS ta ce ta dauki matakin ne bayan dukkan yunkurin da ta yi na tattaunawa ta ruwan sanyi da gwamnatin sojin Nijar din bai yi nasara ba.
Ta ce sojojin na Nijar sun yi watsi da kowanne irin yunkurin shiga tsakanin da suka yi, sannan suka ci gaba tsare hambararren shugaban Nijar, Mohammed Bazoum da iyalansa.
Wani bangare da matsayin kungiyar da aka karanta ya ce, “Mun umarci sashen Manyan Hafsoshin Tsaro na ECOWAS da ya shirya rundunoninmu domin su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.
“Za mu girke dakarun ECOWAS a Nijar domin ganin an dawo da Kundin Tsarin Mulki da gwamnatin farar hula.
“Za mu ci gaba da yunkurin bin wasu hanyoyin na ruwan sanyi don ganin an dawo da mulkin farar hula cikin ruwan sanyi,” in ji ECOWAS.
A ranar 25 ga watan Yulin da ya gabata ne dai sojojin Nijar suka hambarar da gwamnatin Bazoum sannan suka ki amincewa da dukkan wani yunkuri na sasantawa daga ECOWAS da nufin mayar da shi kan karagar mulki.
A baya, ECOWAS ta ba sojojin mako daya su mayar da shi kan mulki ko ta mamaye kasarsu. Sai dai har wa’adin ya kare a karshen makon jiya ba su yi komai a kai ba.