AN ƊAURA AUREN ƊIYAR HON.MAJIGIRI A GARIN MASHI
- Katsina City News
- 08 Sep, 2023
- 964
Yau 08/09/2023.
An ɗaura auren Ɗiyar Zaɓaɓɓen Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Mashi da Dutsi Hon. Salisu Yusuf Majigiri (Garkuwan Gabas Katsina)
An ɗaura auren Khadija Salisu Majigiri da Angonta Arc. Muhammad Adamu Ɗoguru a Babban masallacin juma'a na ke garin Mashi.
Ɗaurin auren ya samu halartar Manyan Manyan baƙi na ciki da wajen jahar nan, akwai manyan yan siyasa,Sarakai,Attajira,Malamai,Yan kasuwa,Yan boko da sauran su
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa PhD shi ne Waliyin Amarya wanda ya bada auren.
Akwai Masoya da magoya baya daga Sassa daban-daban wadanda suka samu shaidar wannan ɗaurin aure mai albarka.