KO GWAMNAN KATSINA NA DA HANNUN WAJEN KOMOWAR GWAMNAN KANO APC?

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12012026_145200_IMG-20260112-WA0053.jpg


Daga Wakilanmu
Katsina Times

Wata hira da Sanata Rufai Sani Hanga, Sanatan da ke wakiltar Kano ta Tsakiya, ya yi da jaridar Weekend Trust a ranar 3 ga Janairu, ta janyo ce-ce-ku-ce kan yiwuwar sauya sheƙar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.

A cewar Sanata Hanga, dagewar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke nunawa kan batun komawa APC na iya kasancewa sakamakon wasu dalilai masu tayar da hankali. Ya ce ana zargin cewa akwai bincike-bincike da Hukumar EFCC ke gudanarwa kan wasu jami’an gwamnatin jihar Kano, inda aka ce an samu wasu da laifuka masu nauyi.

Sanatan ya ƙara da cewa, a cikin zarge-zargen da ake yi, EFCC ta kama wani mutum da ake dangantawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa zargin sayen kadarori na biliyoyin naira, tare da yunƙurin tsare shi domin zurfafa bincike.

Sai dai, Sanata Hanga ya yi zargin cewa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ne ya shiga tsakani, wanda hakan ya sa EFCC ta dakatar da batun tsarewa da kuma ci gaba da binciken.

A cewarsa, idan ba irin wannan dalili ba, yana da wahala Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bar jam’iyyarsa. Ya ce: “Me aka yi masa? Shin mutum zai bar gidan da ya gina da kansa ya koma gidan abokan gaba?”

Hirar ta fito ne tun ranar Asabar, 3 ga Janairu, amma zuwa yau 12 ga Janairu, babu wata sanarwa ko martani daga bangaren Gwamnan Kano, Gwamnan Katsina, ko Hukumar EFCC dangane da zarge-zargen.

Katsina Times
www.katsinatimes.com
Facebook: Katsina City News
Jaridar Taskar Labarai
Dukkan shafukan sada zumunta: Katsina Times
 07043777779

Follow Us