Akalla mutane 300 masu ƙaramin ƙarfi a ƙaramar hukumar Kankia sun amfana da tallafin kuɗi na naira dubu goma-goma daga Shugaban Hukumar Kula da Kadarorin Gwamnatin Jihar Katsina, Lawal Aminu Bala.
Rabon tallafin ya gudana ne a Kankia, awanni kaɗan bayan da aka yi masa sarauta ta Gamjin Kankia na farko, wanda Hakimin Kankia, Alhaji Musa Hassan Sada, ya naɗa shi bisa gudummawar da yake bayarwa ga walwalar al’umma.
A yayin rabon, Dr Lawal Aminu Bala ya bayyana cewa tallafin na daga cikin ƙoƙarin rage wa al'umma raɗaɗin rayuwa, musamman ganin halin tsadar kayayyaki da matsin tattalin arziƙi da ake fuskanta a halin yanzu.
Ya ce irin wannan tallafi yana ƙarfafa zumunci da juna a tsakanin al’umma, tare da bayyana kudirinsa na ci gaba da tsayawa wajen tallafa wa marasa galihu da masu buƙata ta musamman a yankin.
Shugaban hukumar ya kuma yi kira ga sauran masu hali da shugabanni da su mayar da hankali wajen taimakon jama’a, domin haɗin kai ne kaɗai zai taimaka wajen inganta rayuwar al’umma.
Wasu daga cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun bayyana jin daɗinsu, inda suka ce kuɗaɗen sun zo a kan lokaci, kuma za su taimaka musu wajen magance wasu muhimman buƙatun rayuwa. Sun kuma nuna godiya tare da yi masa fatan alheri da nasara a ayyukansa na hidimar jama’a.