Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ya ƙaddamar da aikin gina madatsar ruwa a garin Sabon Layi da ke Karamar Hukumar Ƙanƙara.
Aikin, wanda shirin ACReSAL zai ɗauki nauyinsa, na ɗaya daga cikin muhimman shirye-shiryen samar da ruwa ga dubban mazauna yankin, tare da farfaɗo da tattalin arziƙi musamman a wuraren da matsalolin tsaro suka daɗe suna dagula rayuwa.
Gwamna Radda ya ce aikin na cikin matakan da gwamnati ke ɗauka don dawo da al’amuran yau da kullun a yankunan da suka fama da rashin tsaro. Ya kuma tabbatar wa da al’umma cewa gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan raya kasa a dukkan yankunan jihar.
A nasa jawabin, Kwamishinan Muhalli, Alhaji Hamza Sule Faskari, ya gode wa Gwamna Radda bisa jajircewarsa wajen inganta tsaro da walwalar jama’a. Ya ce ma’aikatarsa za ta ci gaba da bibiyar aikin domin tabbatar da kammalawarsa a kan lokacin.
Shi ma wakilin shirin ACReSAL, Yusha’u Elsunais, ya bayyana cewa dam din zai riƙe akalla cubic metres 700,000, kuma ana sa ran kammala aikin cikin watanni 18.
Shugaban kamfanin da ke aiwatar da aikin, International Consolidated Contractors Offshore da Badawi Azour Trading and Contracting Company, ya tabbatar wa da gwamnati cewa za su yi aiki mai inganci kuma cikin wa’adin da aka gindaya.