Daga Wakilan Katsina Times
Magana da ɓarayin daji ko in ce Fulani masu ɗauke da makamai ya fi komai wahala a bisa tsarin da aka tsara. Mutanen ba su da yarda; kuma suna da gaskiya, saboda suna da ƙarancin ilmin boko, addini ko wayewa, kuma ga su masu aikata laifi ne. Sun yi iƙirarin tuba, amma suna cikin fargaba da rashin tabbas.
Mun tsara bin kasuwanni don magana da su. Da farko mun fara da kasuwannin Jibiya da Batsari, waɗanda a nan ne inda aka fara sulhu, kuma yana tafiya cikin nasara, casa'in bisa ɗari.
A Jibiya bayan kwashe satuttuka, da amfani da duk wata dabara ta kasa samun nasara, dole muka yi amfani da ƙeƙe-da-ƙeƙe. Mun roƙi wani mutum ya yi masu magana in sun amince mu yi magana. Sun amince bisa sharaɗin ba ɗaukar su hoto, ba ɗauka a waya, kuma ba tambayar suna ko inda suka fito.
Bayan mun amince, sun zaɓi zama wani waje a ƙarshen kasuwa bisa tsarin da suka tsara. A nan muka tattauna da su.
Kuna ganin sulhun nan zai ɗore? Zai ɗore idan shugabanninmu suka amince? Amsar da muka samu kenan! Kuna jin daɗin sulhun? "Kwarai kuwa!" Amsar da suka ba da ke nan! Suka ci gaba da cewa, yaƙi, bai da daɗi, kuma zaman lafiya ya fi zama ɗan Sarki! Daga maganar da muka yi da su tabbas sun gaji da faɗan, suna kuma jin daɗin walwalar 'yanci da suka samu. Amma zaman lafiyan ya dogara da bukatar shugabannin su da ke daji.
Mun yi masu tambayar ko ana ɗaukar su haya zuwa kai hare-hare wasu wurare? Suka ce kowane Shugaba yana da yaransa, kuma yaran suna jin maganar shugabannin su. Hari ko kai ɗauki, wannan ya danganta da umarnin shugabannin su.
A kasuwar Batsari, mun kasa nasarar magana da kowa, don babu fuska. Sukan shigo kasuwa cikin gungun mutane huɗu, uku ko biyar, suna yin abin da ya kawo su ne, ba su magana da kowa sai wanda ya shafi abin da za su yi.
Mun yi amfani da wani zagayen mauludi da aka yi a Batsari, wanda aka faɗa mana akwai yiwuwar su zo kallo da shiga mauludin daga daji.
A nan muka yi nasarar magana da wasu. Mun same su cikin annashuwar Maulud da farin ciki. A keɓe, gefe ɗaya bisa sharaɗin ba ɗaukar hoto ko waya, mun tambaye su ya zaman daji? Suka ce lafiya lau, ba fargaba, ba ƙarancin kayan more rayuwa.
Kafin sulhu, kullum akwai tsoron harin jirgi, ga fargabar harin 'yan sa-kai ko sauran jami'an tsaro, ga tsoron idan ɗan uwanmu ya je kasuwa, kila a tare shi.
Ga shi komai za a kai mana a daji, sai an yi sumoga kuma da tsadar gaske.
Daya daga cikin su ya ce, komai ka samu ko kake da shi, in dai kana rayuwar fargaba, ba abin da zai maka daɗi.
Ko sulhun zai ɗore? Watakila wannan magana ce ta ra'ayin shugabannin mu. Su ke da ƙarfi da iko da dajin nan. Su ne ke da makamai, su ke ba mu ko su ba da haya.
Ana zuwa a ɗauke ku haya? Ba za mu ba ka amsar wannan ba.
Kana ganin za ku bari a yi zaɓe? Ya danganta da me shugabannin mu suka ce? Wace jam'iyya za ku zaɓa? Sai abin da aka ce mana. 'Yan siyasa na kai maku ziyara a daji? Ba mu taɓa gani ba, ba kuma mu sani ba; wannan hulɗa ce ta shugabannin mu.
A Batsari, mun yi alƙawari da su za su nema mana lokaci mu shiga dajin, mu gana da shugabannin su da ke yawo cikin dajin. Amma har zuwa rubuta wannnan rahoton ba su kira mu ba a lambar wayar da muka ba su.
Mun yi sati biyu muna zuwa kasuwar 'Yan Tumaki, amma ba mu yi nasarar magana da kowa ba. A 'Yan Tumaki ɓarayin kan zo cikin gungu, kuma ba su hulɗar da ta wuce ta kasuwa da kowa.
Sukan zo kamar su goma, biyar sai su shiga kasuwa, biyar na a wajen mashinan su. In sun dawo, sai sauran su je cin kasuwar. In duk sun gama, sai su duba komai ya kammala na abin da suke son saye?
Kuma suna rarrrabuwa ne, kusan sukan yi ma kasuwar kuri.
Amma ba yadda ba mu yi ba, da duk dubara don a yi magana suka ƙi yarda mu tattauna. A bakin wani masallacin da suka taru suna bin kayan da suka saya, da suka lura wakilan mu suna kwan gaba da dawowa, sai kawai maza-maza suka bar wurin, suka hau baburansu.
Wani mai zama a inda suke haɗuwa ya shaida mana cewa, ai ba su da yarda. Ko sayyaya za su yi, sukan yi a tsararren lokaci ne. Kuma ba sa Hausa a hulɗa da junansu a kasuwa.
A nan muka samu labarin Shugaban ɓarayin yankin . ya taɓa zuwa cikin garin Danmusa yawo, ya zo da eskot ya yi ta gaisawa da mutane.
Wata majiya ta faɗa mana yadda suke zuwa kasuwar Charanci cinikin dabbobi, Mashina da sauran kayan buƙatu. Inda suke zama daban, masu shiga kasuwa daban, masu sa-ido daban. Gaf da tashin kasuwar muka yi magana da wani da ya ce zai ba da haɗin kai, amma a ceci rayuwar sa, kar a bayyana shi. (Munyi hirar tun kafin sulhun Dutsinma, Charanci, Musawa, da Matazu)
Ya rayuwar daji? Ba daɗi. Ba kwanciyar hankali.
Wasu wurare sun yi sulhu, ku fa a nan? Can muke zuwa mu samu sauƙi. Nan ma muna fatan samu don mu samu sa'ida.
A daji, ba abin da ke maka daɗi. In za ka shiga kasuwa sai da dabara. In ka saya, kai shi daji, sai da wayo. Ko ƙara ka ji nesa, sai ka yi tsammanin jirgin yaki ne.
A kasuwar Dutsinma ɓarayin sun yi mu'amala da mutane buɗe. A ranar farko ta shigowarsu kasuwa bayan sulhu, daga nan ba su ƙara ba. Suka koma mu'amalar nawa ne wannan? Sai a biya.
Zuwan mu biyu mun kasa samun da wa za mu yi magana.
ABIN DA MUKA FAHIMTA
Tabbas yanzu ɓarayin daji na neman sulhu, kuma shugabannin su na son hakan. Dalilan da muka gano shi ne, sun gaji, suna kuma neman 'yancin walwala, su kuma ɗan huta. Ko me zai faru bayan an sarara? Wannan lokaci ne zai tabbatar.
Tabbas ɓarayin nan sun shata wani shinge da iyaka wanda suke ganin suke da iko da shi, nasu ne a daji, wanda ya haɗa ƙauyuka da yawa. Kuma komai za a yi a nan sai da izininsu. Haka za a ci gaba da tafiya? Lokaci ne zai tabbatar da hakan.
Tabbas ɓarayin nan, sun kafa wani shugabanci. Wannan shugabancin nasu shi ne zai iya tabbatar da ɗorewar sulhun, ko lalacewarsa. A nan me zai faru idan shugabannin siyasa masu neman ƙuri'a suka fara amfani da waɗannan ɓarayin dajin?