Majalisar Kasa ta amince da nadin Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) daga yankin Arewa ta Tsakiya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya gabatar da sunan Farfesa Amupitan ga Majalisar domin cike gurbin da Farfesa Mahmood Yakubu ya bari bayan kammala wa’adinsa a watan Oktoban 2025.
Farfesa Amupitan, mai shekaru 58, dan asalin garin Ayetoro Gbede a karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi, shi ne mutum na farko daga Arewa ta Tsakiya da aka gabatar domin jagorantar INEC. Yanzu haka yana rike da mukamin Mataimakin Shugaban Jami’ar Jos (bangaren gudanarwa) tare da kasancewa Shugaban kwamitin gudanarwa na Jami’ar Joseph Ayo Babalola da ke jihar Osun.
Farfesa Amupitan kwararren lauya ne wanda aka nada Senior Advocate of Nigeria (SAN) tun a shekarar 2014. Ya kware a fannonin Dokar Kamfanoni, Gudanarwar Kamfanoni, da Dokar Shaida.
Shugaba Tinubu zai tura sunansa zuwa majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatar da nadinsa, kamar yadda doka ta tanada.
Fadar Shugaban Kasa, 9 ga Oktoba, 2025