Hon. Aminu Ibrahim Doguru ya Tallafa da Kayan Makaranta ga Daliban Garo

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02102025_185459_IMG-20251002-WA0328.jpg


Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Majalisa (SLA) ga Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mashi/Dutsi, Hon. Salisu Yusuf Majigiri, wato Hon. Aminu Ibrahim Doguru, ya kaddamar da rabon kayan makaranta ga dalibai a Garin Garo.

Da yake jawabi yayin bikin rabon kayan, Hon. Aminu ya ce an samar da tallafin ne domin bada gudunmawarsa ga ci gaban ilimi tare da rage wa iyaye nauyin kayan makaranta. Ya kara da cewa irin wannan taimako ya dade yana gudanarwa, musamman domin tabbatar da cewa al’umma suna amfana da ci gaban ilimi da sauran abubuwan more rayuwa.

A cewar sa, cikin kayan da aka rabawa daliban akwai notebooks guda 400, pencils 400 da jakunkunan makaranta 400.

Tallafin ya samu karbuwa daga malamai da iyaye a yankin, inda suka bayyana farin cikinsu tare da tabbatar da cewa wannan mataki zai kara karfafa sha’awar karatu da himma ga dalibai.

Follow Us