Gwamna Radda Ya Kaddamar da Littafin Tarihin Fitattun Mutane na Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes01102025_181553_FB_IMG_1759342429727.jpg



Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, 1 Oktoba, 2025

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD, ya bayyana sabon littafi mai taken “Fitattun ’Yan Najeriya sama da 100 daga Jihar Katsina: Tarihi da Gudummawarsu ga Gina Ƙasa” a matsayin tushen tarihi da darasi ga al’ummar zamani da kuma matasa masu tasowa.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a dakin taro na Jami’ar Umaru Musa ’Yar’adua, Katsina, yayin bikin kaddamar da littafin a ranar bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, 1 ga Oktoba, 2025. Littafin, wanda Isaac B. Agbaje da Shehu Sarki Idris suka rubuta, ya tattara tarihin fitattun mutane sama da ɗari daga Katsina da suka taka muhimmiyar rawa a harkokin addini, siyasa, tsaro, ilimi da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

A jawabin sa, Gwamna Radda ya gode wa kwamitin shirya taron da marubutan littafin, yana mai cewa wannan aiki ba wai rubutu kaɗai ba ne, wata gagarumar taska ce ta darasi da koyi ga al’umma.

“Wannan littafi ba kawai littafi ba ne, abu ne da ya kamata mu karanta da zuciya guda, mu yi nazari, mu koyi darasi daga rayuwar wadannan fitattun mutane na Jihar Katsina. Ina fatan matasa za su yi amfani da shi a matsayin jagora,” in ji shi.

Gwamnan ya sanar da cewa ya sayi kwafi goma na littafin domin ’ya’yansa goma, domin kowannensu ya samu abin nazari da koyo. Ya kuma bukaci makarantu da dakunan karatu su tabbatar da cewa littafin ya kasance a hannun matasa domin ilmantar da su.

Radda ya kuma yi tunatarwa da bikin cikar Jihar Katsina shekaru 38 da kafuwa da aka yi a makon da ya gabata, inda ya ce lallai a tuna da jajircewar waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen samar da jihar da ake alfahari da ita a yau.

“Ni da kaina lokacin da aka kirkiro Katsina, ban haura shekaru 18 ba. A yau muna girmama jarumai da suka yi sadaukarwa wajen kafa jihar da muke alfahari da ita,” in ji shi.

Bikin ya samu halartar manyan jami’an gwamnati daga jiha da ƙasa baki ɗaya. Babban Mai Kaddamarwar shi ne Ibrahim Kabir Masari, Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin siyasa, wanda shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Katsina Abdulkadir Mamman Nasiru ya wakilta.

Mai kaddamarwa na Biyu shi ne attajiri Alhaji Dahiru Barau Mangal, yayin da Sanata Ibrahim Ida, Wazirin Katsina, shi ma ya taka rawa wajen kaddamarwar.

Taron ya samu halartar manyan sarakuna ciki har da Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da kauran Katsina Aminu Nuhu Abdulkadir ya wakilta, da Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk Umar. Haka kuma, manyan jami’an tsaro, ’yan siyasa, masana da shugabannin al’umma sun halarci taron.

Littafin ya yi bayani kan gudummawar fitattun ’yan Katsina da suka yi fice a fannoni daban-daban, ciki har da Sheikh Yakubu Yahaya, babban malamin Shi’a, da Sheikh Yakubu Musa Hassan, malamin Ahlus-Sunna, tare da ’yan siyasa, jami’an tsaro, malamai da sauran shugabanni da suka taka rawar gani a tarihin Katsina da Najeriya.

Gwamna Radda ya yaba da wannan littafi, yana mai cewa shi wata hanya ce ta adana tarihi da kuma koyar da darussa na sadaukar wa, Jajircewa da kishin kasa, a karni mai zuwa.

Follow Us