Maryam Jamilu | Katsina Times
Kungiyar Citizens’ Accountability and Governance Forum (CAGF) ta kai kara gaban Hukumar Yaki da cin Hanci da Rashawa da Satar Dukiyar Jama’a (EFCC), tana zargin karkatar da makudan kudaden ayyukan mazabu a mazabar Jibia da Kaita.
A wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a ofishin NUJ, Katsina, a ranar Asabar, shugaban kungiyar, Kwamared Shamsuddeen Salisu Na Alhaji Jibiya, ya bayyana cewa sun nemi a gudanar da bincike na musamman kan dukkanin kudaden ayyukan mazabu daga shekarar 2019 zuwa yau.
Kungiyar ta ce an ware biliyoyin naira domin gina hanyoyi, samar da ruwan sha da suka hada da dam din Jibia, kiwon lafiya, makarantu da shirye-shiryen tallafa wa jama’a. Sai dai, yawancin wadannan ayyuka ko dai ba a aiwatar da su ba, ko kuma an bar su ba'a ida ba, wasu kuma an yi su da farashi fiye da kima ba tare da amfanar jama’a ba.
Takardar karar da EFCC ta karba ta bukaci a yi:
1. Cikakken bincike kan dukkan kudaden ayyukan mazabu na Jibia da Kaita.
2. Bayyana sunayen kwangiloli da masu kwangila.
3. Bincike tare da kwato kudaden da aka karkatar da gurfanar da wadanda aka samu da laifi.
4. Samar da tsarin sa ido daga al’umma kan ayyukan mazabu nan gaba.
Kungiyar CAGF ta jaddada cewa ayyukan mazabu an kitsa su ne domin cike gibin gwamnati da al’umma, ba don amfani wani mutum daya ba.
“Muna tabbatar wa jama’a cewa kungiyar za ta ci gaba da bibiyar wannan kara domin tabbatar da gaskiya, rikon amana da adalci,” in ji sanarwar.
A nasa jawabin, wani mamba daga Kaita, Kwamared Ibrahim Muazu Dankama, ya ce wannan mataki ya zama dole ne sakamakon matsalolin aiwatar da ayyukan mazabu da suka dade suna faruwa a yankin.
“Ba wannan ne karo na farko da ake tura irin wannan koke ba. A baya, Kaita Political Movement Forum ta kai irin wannan kara gaban ICPC,” in ji shi. “Mun yarda lokaci ya yi da za a gudanar da bincike mai zurfi kan yadda ake tafiyar da kudaden mazabu a Jibia da Kaita.”
Kungiyar ta bukaci EFCC da ta dauki mataki cikin gaggawa kan karar tare da tabbatar da gaskiya da nagartar mulki a jihar Katsina.