A SHIYAR FUNTUA | An Gudanar Da Taron Gyara Fasalin Shugabancin Jam'iyar APC A Matakin Mazabu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes16092025_195925_FB_IMG_1758052683731.jpg

‎ Daga Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times.


‎A ranar Talata 16 ga watan Satumba 2025, tawagar jam'iyar APC ta jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin shugaban jam'iyar, Alhaji Sani Ali Ahmad Daura, da kuma mai ba gwamna sharawa akan harkokin siyasa, Hon. Alhaji Umar Ya'u Gwajo-Gwajo, da shugaban jam'iyar na shiyar Funtua Alhaji Ibrahim Danjuma, da kuma mai ba gwamna sharawa akan harkokin yan majalisu Hon. Nasiru Ala Iyatawa.
‎Sannan kuma a cikin tawagar akwai Ma'ajin jam'iyar, Hon. Alhaji Hassan, da kuma mai ba gwamna sharawa akan harkokin mata na shiyar Funtua Hajiya Jamila, da majidadin jam'iyar tare da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a matakin shiyar Funtua, sun kai ziyara ta musamman a kananan hukumomin Kankara, Malumfashi, Musawa, Matazu, domin gyara fasalin jam'iyar a matakin mazabu.
‎A yayin ziyarar shugaban jam'iyar APC Alhaji Sani Ali Ahmad Daura ya bayyana makasudin ziyarar tasu, itace gyara fasalin shugabancin jam'iyyar a matakin mazabu. Gabatar da ayyukan da gwamna Malam Dikko Umar Radda ya yi ma jihar Katsina a shekaru biyu na mulkin shi. Gabatar da umarnin da gwamna ya yi na shugaban karamar hukuma ya dauki mutum hamsin aiki a matsayin masu taimaka mashi a harkoki daban-daban.
‎"Malam Dikko Umar Radda ba abin da ya sanya gaba kamar yaga an samu zaman lafiya a jihar nan, kullum abin da yake damunsa itace matsalar tsaro a jihar nan da abin yake kwaciya kuma dashi yake tashi a koda yaushe. Ya kawo tsaruka daban-daban domin ganin an samar da hanyar da za a magance matsalar tsaro a jihar." inji shi.
‎Ya kara da cewa jam'iyar APC a matakin jiha bata yarda da tallata wani dan takara ba walau yana kan mulki ne ko baya kai, yace yanzu ba lokacin yakin neman zabe bane, lokaci ne na yi ma mutane ayyuka, ya kara da cewa jam'iyar APC a matakin jiha zata dauki mataki mai tsauri akan duk wanda ta kama da laifin.
‎"Shugabannin jam'iyar APC ku sani, baya hallata a yanzu shugaban jam'iyar ya rinka yawon tallar wani dan takara ba, walau yana kan kujerar mukami ko akasin haka. Duk shugaban jam'iyar da aka kama ya shiga wannan halin na yakin neman zaben wani, to jam'iyar APC a matakin jiha zata hukunta shi. Ku iyaye ne ku tsaya a matsayin ku har zuwa lokacin da za a bayyana wanda za a goya ma baya" inji shi.
‎"A yanzu akwai shugabannin rumfa da za a yi mutum tara tara, kuma a cikin tarar za a sanya mace guda uku a ciki duba da irin rawar da mata suke badawa a wajen zabe, kuma sannan ana son a bayar da sunayen tarar nan, nan da sati guda, kuma dole kowane daga cikin su ya kasance yana da katin zabe da kuma katin zama cikakken dan jami'ya." Inji shi.
‎"Akwai kuma tsari da gwamna ya kawo ga shugabannin kananan hukumomi na daukar mutum hamsin aiki, bangaren ciyaman da kawuncil su bada mutum ashirin, sai masu ruwa da tsaki na jam'iyar da masu bada shawara mutum talatin, a cikin talatin din nan ana so a sanya mace biyar, sai maza ashirin da biyar, ana so a sanya matasa a ciki domin a tafi tare dasu." inji shi.
‎A ta bangaren shugabannin kananan hukumomin da shugabannin jam'iyun sun yaba da wannan sabon tsari da jami'yar a matakin jiha ta kawo, da kuma umarnin da gwamna ya yi na daukar mutum hamsin aiki, sannan sun bayyana jin dadin su a yadda uwar jam'iyar ke yin aiki tukuru na ganin ta samar da hadin kai a tsakanin dukkan yan jam'iyar.

Follow Us