An Gudanar da Taron Sulhu Tsakanin ’Yan Bindiga da Al’ummar Faskari a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes15092025_140505_IMG-20250506-WA0180.jpg

Auwal Isah Musa, Zaharaddeen Ishaq Abubakar (KatsinaTimes)



An gudanar da taron tattaunawa tsakanin shugabannin al’umma da kuma jagororin ’yan bindiga a garin Bilbis, karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, a ranar Lahadi, domin kawo ƙarshen rikice-rikicen da suka addabi yankin tsawon shekaru.

Taron ya samu halartar Masu Sarautun gargajiya da dagatai da masu unguwanni, ciki har da Hakimin Faskari, Injiniya Aminu Tukur Sa’idu da Sarkin Yamman Katsina Hakimin Mairuwa, Alhaji Sani Sabo Idris. Haka kuma fitattun shugabannin ’yan bindiga sun halarta, ciki har da shahararren jagoran da hukumomin tsaro suka daɗe suna nema ruwa a jallo, Alhaji Ado Aleru.

A jawabinsa, Hakimin Faskari ya bayyana wannan mataki a matsayin “hanya mai muhimmanci da za ta kawo ƙarshen matsalar tsaro,” yana mai addu’ar Allah ya tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Daga bangaren ’yan bindiga, Hassan Magazu ya yi korafi kan rahotannin da ake yadawa daga kasashen waje, yana mai kiran hakan rashin adalci. “Ku dawo gida ku ga irin wahalhalun da ake ciki, ku taimaka wajen kawo karshensa, ba wai ku zauna a waje kuna rubuce-rubuce ba,” in ji shi.

Wani shugaban su, Isiya Kwashe, ya ce kabilanci ya tsananta rikicin, ya kuma yi gargadin cewa babu zaman lafiya na gaskiya sai an dawo da adalci. A nasa bangaren, babban jagoran su, Alhaji Ado Aleru, ya bayyana cewa wannan sulhu zai dawo da zumunci tsakanin Fulani da Hausawa, tare da tabbatar da cewa yarjejeniyar ba ta tsaya ga Faskari kawai ba, har ma za ta iya shafar wasu sassan Najeriya.

Sarkin Rafin Katsina, Hakimin Mairuwa, ya tunatar da yadda a baya Fulani da sauran al’umma ke rayuwa lafiya tare, yana mai kiran jama’a da su haɗa kai don dawo da zaman lafiya.

Taron ya kammala da addu’o’i na neman dorewar zaman lafiya a Faskari, Katsina da ma Najeriya baki ɗaya.

A nata bangaren gwamnati, Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya bayyana matsayinsa kan irin waɗannan yarjejeniyoyi. A cikin wani shiri na Conflict Prevention, Crisis Response and Resilience (CPCRR) na Tarayyar Turai (EU) da ake aiwatarwa a Katsina da Zamfara, gwamnan ya ce ba zai fara zaman sulhu da ’yan bindiga ba sai sun fara ajiye makamai bayan sun fuskanci matsin lamba daga rundunar tsaro.

“Zan yi sulhu da su ne kawai idan sun nemi hakan da kansu bayan sun ji wuta a wajen dakarun tsaro. Gwamnati kuma za ta tallafa wa wadanda suka yi fama da matsalar, da ma wadanda suka tuba suka ajiye makaman su,” in ji gwamna Radda.

Shirin CPCRR na Tarayyar Turai (EU) na mai da hankali kan hana rikici, magance matsalolin gaggawa, da gina ƙarfin juriya a cikin al’umma, tare da taimakawa wajen daidaitawa da kuma sake haɗa wadanda suka tuba cikin rayuwar yau da kullum.

Wannan taron sulhun a Faskari ya zama ɗaya daga kananan hukumomin bakwai da suka rungumi irin sa, da suka hada da Jibiya, Batsari, Kankara, Kurfi, Danmusa, Safana da Faskari tare da fatan shirin yaci gaba zuwa sauran kananan hukumomin da matsalar daki ci taki cinye wa.

Follow Us